Albashin N21m: Majalisa Ta Bayyana Gaskiyar Abin da Ake Biyan Sanatoci

Albashin N21m: Majalisa Ta Bayyana Gaskiyar Abin da Ake Biyan Sanatoci

  • Majalisar dattawa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da alawus-alawus duk ƙarshen wata
  • Kakakin majalisar, Adeyemi Adaramodu ya bayyana cewa kudin da Kawu Sumaila ya yi iƙirarin ana ba shi ba albashi ba ne
  • Sanata Adeyemi Adaramodu ya yi nuni da cewa kuɗin gudanarwa ne domin ayyukan ofis inda ya ce albashin sanatocin N1m ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da kuɗin alawus-alawus.

Majalisar dattawan ta musanta hakan ne a ranar Alhamis, biyo bayan kalaman da Sanata Kawu Sumaila ya yi na cewa yana samun kusan N22m duk wata.

Majalisa ta fadi albashin sanatoci
Majalisa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Majalisa ta yi ƙarin haske kan albashin sanatoci

Kara karanta wannan

Bayan fadin albashin sanatoci, Kawu Sumaila ya yi sabuwar fallasa

Kakakin majalisar dattawan, Sanata Adeyemi Adaramodu ya yi ƙarin haske kan lamarin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar Adaramodu ya yi ƙarin haske kan iƙirarin da sanata Kawu Sumaila ya yi na cewa ana ba shi N21m a matsayin kuɗin gudanarwa bayan albashin da ake ba shi na N1m.

Sai dai, Adaramodu ya bayyana cewa cewa kuɗien gudanarwa daban suke da albashi da alawus ɗin ƴan majalisar.

Ya bayyana cewa hukumar RMAFC ce ta ƙayyade albashin sanatocin wanda yake a matsayin N1,063,860:00 duk wata.

"Kuɗin gudanarwa ne ba albashi ba" - Majalisa

Adaramodu ya bayyana cewa ba majalisar kaɗai ake ba kuɗaɗen gudanarwa ba.

"Dukkanin ɓangarorin gwamnati da ma'aikatansu, gwamnoni, ministoci, manyan sakatarori, kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi suna gudanar da ayyukansu ne da kuɗaɗen gudanarwa. Hakan yake a majalisar dattawa."

Kara karanta wannan

Bayan fallasar Kawu Sumaila, an gano albashin da sanatoci ke lakumewa duk wata

"Saboda haka kuɗaɗen da Sanata Kawu Sumaila yake magana a kai ba albashinsa ba ne ko kuɗin alawus."
"Kuɗin gudanarwa ne na yin ayyukan ofis da kula da ma'aikata. Kuɗaden sun kuma ƙunshi na yin ayyuka a mazaɓu."

- Sanata Adeyemi Adaramodu

Albashin sanatoci a kowane wata

A wani labarin kuma, kun ji cewa bincike ya nuna cewa sanatoci 99 da ke a majalisar dattawan Najeriya na ƙarɓar albashin N2bn duk ƙarshen wata.

Wannan jimillar kuɗin albashin bai ƙunshi abin da ake biyan shugabannin majalisar ba waɗanda har yanzu ba a san adadin abin da suke samu ba duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng