Tallafin Karatu: EFCC Ta ba da Gudummawar N50bn ga Asusun NELFUND? Bayanai sun Fito
- Hukumar EFCC ta musanta ba da gudummawar Naira biliyan 50 ga asusun ba da lamunin karatu ga daliban manyan makarantu (NELFUND)
- EFCC mai yaki da cin hanci da rashawar ta ce Naira biliyan 50 da aka turawa asusun domin tallafa wa shirin ba gudumawa ce daga EFCC ba
- Hukumar kasar ta kuma bayyana cewa ba ta da hurumin tantance inda gwamnatin tarayya ke amfani da kudin laifukan da aka kwato
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta ce Naira biliyan 50 da aka tura cikin asusun ba da lamunin karatu na Najeriya (NELFUND) ba gudummawa ba ce.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta ce kudin ba ba gudumawa ba ce, amma wani bangare ne na kudaden laifuffuka da aka kwato wanda aka turawa gwamnatin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken “N50bn da EFCC ta turawa NELFUND ba gudunmawa ba ce” da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta magantu kan turawa NELFUND kudi
EFCC ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya yanke shawarar saka kudin domin tafiyar da babban shirin gwamnatinsa na ba da rance ga dalibai.
Hukumar ta ci gaba da cewa, ba ta da hurumin tantance inda gwamnatin tarayya ke amfani da kudaden sata da aka kwato.
A cewar sanarwar, EFCC ta ce ta yi imanin cewa ba da lamunin karatu wani babban shiri ne da ke da damar rage yawan shigar matasa a cikin aikata laifuffuka.
Sanarwar da hukumar EFCC ta fitar
Duba sanarwar a nan kasa:
Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta sha alwashin sanya ido kan yadda ake amfani da kudaden domin tabbatar da bin diddigi da kuma cimma manufofin shirin.
NELFUND: An samu karin makarantun jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa asusun ba da lamunin karatu na NELFund ya ce ya tantance karin manyan makarantu 22 mallakar jihohi domin ba dalibansu rancen kudi.
A wata sanarwa da asusun ya fitar yau, ya ce daliban manyan makarantun 22 za su iya neman rancen kudin a yanzu bayan da kwamitin tantance makarantu ya amince da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng