Da Dumi-Dumi: An Dawo da £4.2m Zuwa Najeriya, Kudaden Da Ibori Ya Sace
- Gwamnatin tarayya ta yi nasarar karbar kudaden da Ibori ya sace ya boye a kasar waje
- Ministan shari'a ne ya jagoranci karbar kudin daga kasar wajen Ibori ya kai kudaden ya boye
- Gwamnati ta bayyana adadin kudaden tare da bayyana inda aka ajiye su ga manema labarai
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karbi £4,214,017.66 na almundahanar da ke da alaka dangin tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori.
Umar Gwandu, mai taimakawa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ofishin Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Talata, in ji Channels Tv.
KU KARANTA: Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja
A cewar sanarwar an sanya kudin a cikin asusun da aka ware na Gwamnatin Tarayya tare da darajar Naira daidai da kudin ya zuwa 10 ga Mayu, 2021.
Mista Malami ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don dawo da dukiyar da Ibori ya sace zuwa gida Najeriya a madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Daily Trust ta ce Gwamnatin jihar Delta ta yi zanga-zangar cewa ya kamata a mayar da kudin zuwa jiharta.
KU KARANTA: NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudurta sake cin bashin N2.342trn don gudanar da wasu ayyuka a Najeriya.
Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Ahmed Lawan ne ya karanta takardar da shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar a zamansu na yau Talata 18 ga watan mayu.
Legit.ng Hausa ta gano majalisar dattawan Najeriya ta wallafa bukatar shugaban kasan a shafin Twitter cewa shugaba Buhari na mika , "Kudurin Majalisar Kasa don aiwatar da karbar bashin waje na dala biliyan 2.18 a cikin Dokar Kasafin Kudin 2021"
Asali: Legit.ng