Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ragargaji Abba kan ‘Sakacin’ Sace Takardun Shari’ar Ganduje

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ragargaji Abba kan ‘Sakacin’ Sace Takardun Shari’ar Ganduje

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na shan kakkausar suka kan sace takardun shari'ar shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje
  • Tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano, Muaz Magaji na cikin waɗanda suka yi martani mai zafi ga gwamna Abba kan lamarin
  • A jiya Laraba ne gwamna Abba ya sanar da cewa an sace takardun shari'ar a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano na cigaba da shan suka daga mutane daban daban kan sace takardun shari'ar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa an sace takardun shari'ar ne a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Abba Kabir Yusuf
An yiwa Abba Kabir martani kan sace takardun shari'ar Ganduje a kotu. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shari'ar Ganduje: Martanin Muaz Magaji

Tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muaz Magaji ya wallafa martani kan lamarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muaz Magaji ya ce sakaci ne babba a ce an shiga har ofis an sace takardun da ake shari'ar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Tsohon kwamishinan ya yi nasiha ga Abba Kabir Yusuf inda ya ce gwamnan ya tuna cewa hakkin al'umma ne a kansa saboda haka ya kiyaye amana.

Sowore ya yi martani kan takardun Ganduje

Dan jarida mai rajin kare hakkin dan Adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore na cikin waɗanda suka soki gwamnatin.

Omoyele Sowore ya wallafa martani ga Abba Kabir Yusuf a shafin X inda ya ce sai Abba ya nemi takardun a wajen Dan Bello.

Omoyele Sowore ya ce abin ya zama kamar wasan yara yadda ake samun sakaci a wurare masu muhimmanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi bayan kotun turai ta saka Najeriya a gaba kan jirage 3

Ya kuma kara da cewa ya kamata ace akwai wasu takardun a wajen lauyoyin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shari'a ta yadda ɓatan ba zai tada hankali ba.

An lalata dukiyar N1bn a kotun Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana irin asarar da ake zargi yan daba sun yi a ma'aikatar shari'ar jihar a lokacin zanga zanga.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido ma'aikatar shari'ar Kano domin ganewa idonsa muguwar barnar da aka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng