Kwanaki Bayan Buhari Ya Gana da Tinubu, Sheikh Pantami Ya Samu Babban Matsayi

Kwanaki Bayan Buhari Ya Gana da Tinubu, Sheikh Pantami Ya Samu Babban Matsayi

  • Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya samu matsayi a ƙungiyar hadin kan Afrika
  • Sheikh Isa Ali Pantami ya samu matsayin ne tare da wasu jiga jigan masana daga sassa daban daban na yankunan Afrika
  • Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da shugaba Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar hadin kan kasashen Afirka (AU) ta gwangwace Sheikh Isa Ali Pantami da babban matsayi.

Sheikh Isa Ali Pantami ya samu matsayin ne kwanaki biyu bayan Muhammadu Buhari ya gana da Bola Tinubu a taron majalisar magabatan kasa.

Kara karanta wannan

Cin hanci: Ganduje ka iya rasa kujerarsa, watakila Tinubu ya sauya masa mukami

Sheikh Pantami
Sheikh Pantami ya samu matsayi a kungiyar AU. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Legit ta gano lamarin ne a cikin wani sako da Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis, 15 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganawar Buhari da Tinubu a Abuja

Legit ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma fadar shugaban kasa yayin taron majalisar magabatan Najeriya domin ganawa da Tinubu.

Sheikh Isa Ali Pantami na cikin mutanen da suka raka Muhammadu Buhari fadar shugaban kasa yayin zaman.

AU ta ba Sheikh Isa Pantami matsayi

Kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta ba Sheikh Pantami matsayin jagorancin hadin gwiwa na kirkira da fasaha.

Ana sa ran cewa Sheikh Pantami da sauran jagororin za su kawo tsarin da kasashen Afrika 54 za su bi wajen inganta fasahar zamani.

Abokan aikin Sheikh Pantami a AU

Daga cikin wanda za su yi jagoranci tare da Sheikh Pantami akwai Farfesa Anicia Nicola daga ƙasar Namibia.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Karin masana sun hada da Farfesa Khaleed Ghedira daga Tunisia, Farfesa Maha Grima daga Morocco sai Farfesa Mongi Nouira da Farfesa Munir Frija.

Sheikh Pantami ya yi rashin kawu

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin musulunci, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin mutuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu.

Tsohon ministan Najeriyan ya ce kawun nasa wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu ne yana da shekaru 110 a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng