Zanga Zanga: Akpabio, Sanatan Kano da Sauran Manyan da Suka Yi wa 'Yan kasa Izgili

Zanga Zanga: Akpabio, Sanatan Kano da Sauran Manyan da Suka Yi wa 'Yan kasa Izgili

Zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki hankalin kasa, ganin duk kokarin hana fitowa ya ci tura.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Zanga-zanga ta kwanaki 10 da 'yan kasar nan su ka gudanar ya bankado yadda wasu jagorori ke kallon talakawa. Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio na gaba-gaba a wannan mataki, domin har bakar magana ya jefa ga masu shirin zanga-zanga.

Hanga
Shugabannin kasar nan sun rika gayawa masu zanga-zanga bakaken maganganu Hoto: Rufa'i Hanga Sanata/ Nigerian Senate
Asali: Facebook

Legit ta tattaro ma ku kalaman wasu shugabanni gabanin fara zanga-zanga yunwa a kasar nan:

1. "Ba mu san dalilin zanga-zanga ba" - Gwamnoni

Kara karanta wannan

Matasa miliyan 1 za su yi tattakin goyon bayan Tinubu bayan zanga zangar adawa

Gwamnonin Najeriya sun ba wa jama'a mamaki bayan sun furta cewa ba su ma ga dalilin da zai sa 'yan kasar nan zanga-zanga ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin APC ta bakin shugabansu, Hope Uzodinma suka fadi haka duk da kukan wayyo Allah da 'yan kasa ke yi, Daily Trust ta wallafa.

2. "Ana zanga-zanga, mu na cin abinci" - Akpabio

Premium Times ta wallafa yadda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jefa mummunan kalami ga masu shirin fita zanga-zangar adawa da matsin rayuwa. Apbabio na ganin tun da 'yan Najeriya sun dage sai sun yi zanga-zanga, su je su yi ta yi, su kuma su na gefe cikin kwanciyar rai su na cin abinci.

3. "Ni ma yunwa na ke ji" Sanata Hanga

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar kasa ya jawo ɓaɓatu bayan ya ce shi ma yunwar da 'yan kasar nan ke ji, ita ya ke ji. Wani mai amfani da shafin Facebook, Sani Dauda Dahiru ya wallafa bidiyon Sanatan ya na cewa "Ni ma ina bukatar dauki."

Kara karanta wannan

Kano: Mabarata sun shafe kwanaki da yunwa, sun nemi a janye zanga zanga

5. Gwamna Radda: An dauki nauyin zanga-zanga

Duk da gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda na magana ne kamar ya na goyon bayan yan kasa, amma ya ce daukar nauyin matasan aka yi, TRT ta wallafa. A wani bidiyo na daban kuma da Sier Ahmad Tatah ya wallafa a shafin Facebook, an ji gwamnan yana sukar masu fafutukar karin albashi. A cewar gwamnan, mai sayar da taliyar yara sai yafi ma'aikacin gwamnati samu ko da an kara albashi zuwa N60,000.

Zanga-zanga: Kalaman Akpabio ya harzuka matasa

A baya kun samu labarin yadda kalaman shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bakantawa matasan kasar nan ganin cewa su na kuka ne ga manufofin gwamnati.

Tuni matasan su ka rika zafafan martani, har da masu neman a yiwa shugaban kiranye, inda ake ganin abu ne mai yiwuwa matukar matasan za su jajirce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.