Hankalin Tinubu Ya Tashi Bayan Kotun Turai ta Saka Najeriya a Gaba kan Jirage 3

Hankalin Tinubu Ya Tashi Bayan Kotun Turai ta Saka Najeriya a Gaba kan Jirage 3

  • Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan wani kamfani a kasar Sin ya samu izinin kwace jiragen shugaban ƙasa guda uku
  • Mai taimakawa shugaban kasa a harkokin sadarwa, Dada Olusegun ne ya fitar da sanarwar a yau bayan labarin ya baza duniya
  • Haka zalika Dada Olusegun ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu take wajen ganin ta shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa cikin gaggawa bayan wani kamfani ya samu izinin kotu domin kwace jiragen shugaban kasa.

An ruwaito cewa rikici ne ya faru tsakanin gwamnatin jihar Ogun da wani kamfani a kasar Sin wanda lamarin har ya kai ga haka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kuma gamuwa da cikas bayan kwace jiragen fadar shugaban kasa 3 a ketare

Jirgin Najeriya
Gwamnati ta yi martani kan kwace jiragen shugaban kasa. Hoto: Nigerian Air Force HQ.
Asali: Facebook

Legit ta gano kokarin da fadar shugaban kasa take yi kan lamarin cikin sakon da Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar kwace jiragen shugaban ƙasa 3

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gwamnatin Ogun ta yi yarjejeniya da kamfanin Zhongshan Fucheng na kasar Sin.

Amma sai aka samu tangarɗa kan yarjejeniyar da kamfanin ya kulla da gwamnatin a 2016 kuma sai ya tafi kotu domin neman kwace jiragen shugaban kasa kan sabanin da suka samu.

Jawabin fadar shugaban kasa kan kwace jirage

Gwamnatin tarayya ta ce tana sane da shirin kamfanin Zhongshan Fucheng na neman kwace kadarorin Najeriya.

Sai dai fadar shugaban kasa ta ce ba ta da wata alaƙa da kamfanin da zai nemi kwace kadarorin Najeriya.

Haka zalika gwamnatin ta ce ba a sanar da ita kan maganar kwace jiragen ba kawai ita ma a sama ta ji labarin.

Kara karanta wannan

Babu haraji: Bayani dalla dalla kan sharuddan shigo da abinci Najeriya kyauta

Kokarin gwamnati kan sasanta rikicin

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kokarin ganin samun daidaito tsakanin gwamnatin Ogun da kamfanin Zhongshan Fucheng domin kashe wutar rikicin.

Kamfanin Zhongshan Fucheng ya samu izinin kotu ne daga Faris kan kwace jiragen tun a watan Maris na wannar shekarar.

Za a sayar da jiragen shugaban kasa

A wani rahoton, kun ji cewa an sanya wasu tsofaffin jiragen shugaban ƙasa guda uku na gwamnatin tarayyar Najeriya a kasuwa.

An tattaro cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin sayar da jiragen saboda kuɗaɗen da ake kashewa wajen kula da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng