Bayan Fadin Albashin Sanatoci, Kawu Sumaila Ya Yi Sabuwar Fallasa
- Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya zargi tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Aremu Obasanjo da kawo cin hanci da rashawa a majalisa
- Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu ya bayyana cewa Obasanjo ya kawo cin hanci a majalisar domin cimma ƙudirinsa na yin tazarce a karo na uku
- Kalaman na Kawu Sumaila na zuwa ne a matsayin martani kan zargin da Obasanjo ya yi na cewa ƴan majalisar tarayya suna yanke abin da za a biya su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya zargi tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da kawo cin hanci da rashawa a majalisar tarayya.
A makon da ya gabata ne Obasanjo ya zargi ƴan majalisun da ƙayyade albashi da alawus-alawus ɗinsu da kansu a yayin da ake fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a Najeriya.
Kawu Sumaila ya caccaki Olusegun Obasanjo
A yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Alhamis, Kawu Sumaila ya caccaki kalaman na Olusegun Obasanjo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan wanda ya fito ya bayyana abin da ake ba shi duk wata a matsayin albashi, ya zargi Obasanjo da gurɓata wasu ƴan majalisa ta hanyar ba su cin hanci a lokacin mulkinsa.
Wane zargi Kawu Sumaila ya yi kan Obasanjo?
"Idan ana magana kan cin hanci da rashawa, Obasanjo ne ya kawo cin hanci a majalisar dokoki ta tarayya."
"Ina da shaida saboda gwamnatinsa da wasu na kusa da shi ne suka gurɓata wasu ƴan majalisun tarayya domin su yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin ya samu damar yin tazarce."
- Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila
Ɓoye haƙiƙanin abin da ake biyan sanatocin a matsayin albashi da alawus dai ya zama abin magana inda ake ta tafka muhawara a kai.
Albashin da ake biyan sanatoci duk wata
A wani labarin kuma, kun ji cewa alamu sun nuna cewa adadin albashin da ake biyan sanatoci 99 na majalisar dattawan Najeriya duk wata ya haura N2bn.
Wannan adadin bai ƙunshi albashin da ake biyan shugabannin majalisar su 10 ba, waɗanda har yanzu ba a san abin da suke karɓa ba duk wata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng