An Yanke N10m a Matsayin Kudin Shiga Takarar Zaben Kananan Hukumomin Kano

An Yanke N10m a Matsayin Kudin Shiga Takarar Zaben Kananan Hukumomin Kano

  • Hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta bayyana kudin neman takarar shugabannin kananan hukumomi da kansiloli
  • Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi ya ce duk mai son tsayawa takarar shugaban karamar hukuma zai ajiye N10m
  • Farfesa Malumfashi ya kuma ce wadanda ke sha'awar tsayawa takarar kansila za su sayi takardar tsayawa takara a N5m

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC), ta fitar da kudin sayen takardar tsayawa takara ga shugabanni da kansilolin karamar hukuma.

KANSIEC ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan kananan hukumomi 44 a ranar 30 Nuwamba, 2024 domin maye gurbin shugabannin riko a jihar.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya ragargaji Abba kan 'sakacin' sace takardun shari'ar Ganduje

Abba Kabir Yusuf
Hukumar zabe ta sanya N10m a matsayin kudin neman takarar shugaban karamar hukuma a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi ya ce masu sha'awar zama shugabannin kananan hukumomi za su biya N10m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su kuma masu sha'awar tsayawa takarar kansila za su sayi takardar nuna sha'awar fitowa takarar a kan N5m, Daily Trust ta wallafa.

"Ba ni da alaka da jam'iyyu," Shugaban KANSIEC

Shugaban hukumar zabe ta Kano, Farfesa Sani Malumfashi ya jaddada cewa ba shi wata alaka da dukkanin jam'iyyun da ke jihar Kano.

Ya fadi haka ne a ranar Alhamis a wani yunkuri na tabbatar da cewa ba zai amince da murdiya a zaben kananan hukumomi da za a yi ba.

"Shirin KANSIEC zai dakile takarar wasu," CISLAC

Kungiyar da ke rajin inganta ayyukan majalisu (CISLAC), ta yi Allah wadai da yawan kudin da hukumar KANSIEC ta sanya na tsayawa takara a kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

Shugaban hukumar, Auwal Musa Rafsanjani ya shaidawa Legit cewa yawan kudin zai hana masu kudin halak da masu gaskiya neman takara.

Dan takarar NNPC ya yi nasara a zabe

A baya kun samu labarin yadda dan takarar kansila a jam'iyyar NNPP ya yi nasara a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar Adamawa.

Shugaban hukumar zabe a jihar, Mohammed Umar ya ce jam'iyya mai mulki ta PDP ce ta yi nasarar lashe zaben dukkanin kujerun shugabancin kananan hukumomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.