Rikici ya Ɓarke a APC Bayan Ta Rabu Gida 2 a Jihar Arewa, Gwamna Ya yi Gargadi

Rikici ya Ɓarke a APC Bayan Ta Rabu Gida 2 a Jihar Arewa, Gwamna Ya yi Gargadi

  • Rikicin shugabancin jam'iyya ya kara ƙamari a jihar Benue yayin da ɓangare daya ya nufi yin taron masu ruwa da tsaki a yau Alhamis
  • Gwamnan Benue Hyacinth Alia ya gargadi ɓangaren da suke shirin shirya taron kan kaucewa tayar da fitina a jihar saboda siyasa
  • Tun a watan Janairun shekarar 2024 rikici ya bulla a APC a Benue inda gwamnan jihar da Sanata George Akume suke takun saƙa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rikicin APC ya kara ƙamari yayin da ɓangaren da ya zama kishiya ga gwamnan jihar ya shirya taro.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya gargadi ɓangaren da suke shirin shirya taro ba tare da izinin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Gwamna Alia
Gwamna Alia ya gargadi masu shirya taron APC. Hoto: Tersoo Kula
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan gargadin da gwamna Alia ya yi ne a cikin sakon da jami'in yada labaransa, Tersoo Kula ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC za ta shirya taro a Benue

Jami'in yada labaran gwamnatin jihar ya bayyana cewa sun samu labarin cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC, Austin Agada ya shirya taron jam'iyya.

Gwamnatin Benue ta yi zargin cewa an shirya taron ne a yau Alhamis, 15 ga watan Agusta kuma ya sabawa doka.

Gwamna Alia bai san da taron APC ba

Gwamna Hyacinth Alia ya ce a matsayinsa na jagoran jam'iyyar APC a jihar bai san da wani taro ba.

Ya kuma tabbatar da cewa a matsayinsa na mai alhakin samar da tsaro a jihar dole a sanar da shi duk wani taro da za a yi.

Taron APC: Gwamna Alia ya yi gargadi

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Gwamna Hyacinth Alia ya ce a jihar Benue akwai doka da oda saboda haka ba wani taro da za a shirya ba tare da bin ka'ida ba.

Saboda haka ya gargadi duk wanda yake shirin tayar da fitina a jihar ya shiga hankalinsa saboda doka za ta yi aiki a kansa ko shi waye.

Ricikin APC ya barke a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin cikin gida ya sake kunno kai a cikin APC yayin da Kabiru Marafa ya sanar da dawowar wani tsagin jam'iyyar.

Tsohon sanatan na Zamfara ta tsakiya ya ce ya farfado da tsagin jam'iyyar ne saboda ya fahimci an cire shi daga sabgar APC a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng