An Gano Abin da Yarjejeniyar Najeriya da Kasar Equatorial Guinea Ta Kunsa

An Gano Abin da Yarjejeniyar Najeriya da Kasar Equatorial Guinea Ta Kunsa

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Equatorial Guinea, Nguema Mbasogo sun rattaba hannu a yarjejeniya
  • Shugaban kasar nan, Tinubu ya ce hadin gwiwar kasashen biyu zai habaka samar da ayyukan yi da sashen iskar gas
  • Haka kuma shugabannin biyu sun tattauna muhimman batutuwa da su ka shafi tsaro, samar da ayyukan yi da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Equatorial Guinea - Najeriya ta shiga yarjejeniya da gwamnatin Equatorial Guinea a kan aikin bututun iskar gas na Golf Guinea.

Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Equatorial Guinea,Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ne su ka sanya hannu kan yarjeniyar.

Kara karanta wannan

Cutar kyandar biri ta bulla Congo da wasu kasashen Afrika, WHO ta fitar da bidiyo

Bola Tinubu
Najeriya da Guinea sun shiga yarjejeniya kan iskar gas Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

A sakon da ofishin yada labaran shugaban kasa ya wallafa a shafin X, yarjejeniyar za ta habaka samar da aikin yi da saukaka safarar iskar gas tsakanin kasashe da ke yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alfanun yarjejeniyar gas tsakanin Najeriya & Equatorial Guinea

Gwamnatin kasar nan ta bayyana cewa yarjejeniya samar da bututun iskar gas da Guinea zai samar da ayyukan yi tsakanin 'yan kasashen biyu.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa yarjejeniyar za ta bude kofar cin moriyar albarkar sashen iskar gas, hadiminsa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafin Facebook.

Abubuwan da aka tattauna a taron Najeriya-Equatorial Guinea

Sauran abubuwa da shugabannin Najeriya da Guinea su ka tattauna sun hada da samar da wadatar abinci, samar da ayyuka, hadin gwiwa da hanyoyin warware matsalolin tsaro. A jawabinsa, shugaban kasar Guinea, Nguema Mbasogo ya ce yarjejeniyar za ta tabbatar da cigaba a nahiyar Afrika ba ki daya.

Kara karanta wannan

Babu haraji: Bayani dalla dalla kan sharuddan shigo da abinci Najeriya kyauta

Mista Mbasogo ya kuma ce za su hada kai da Najeriya wajen samawa Afrika gurbi na dindindin a majalisar dinkin duniya.

Shugaba Tinubu zai kai ziyarar aiki Equatorial Guinea

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar Equatorial Guinea a ziyarar aiki ta kwanaki uku jim.kadan bayan kammala zanga-zanga.

Hadimin shugaban Tinubu, Ajuri Ngelale ya ce shugaban ya tafi Equatorial Guinea ne domin mutunta gayyatar da shugaban kasar, Obiang Nguema ya yi masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.