Mata Sun Fantsama Tituna Tsirara Domin Yin Zanga Zanga, Basarake Ya Rarrashe Su

Mata Sun Fantsama Tituna Tsirara Domin Yin Zanga Zanga, Basarake Ya Rarrashe Su

  • Daruruwan mata ne suka fito kan tituna tsirara domin nuna damuwa kan kisan gilla da makiyaya ke yi musu a gonaki
  • Matan wadanda mafi yawansu dattawa ne sun fito kan tituna ne a yankin Akoko da ke jihar Ondo saboda rashin tsaro
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin wani makiyayi da kisan manomi da karensa a cikin gonarsa a karshen mako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Wasu mata sun fantsama kan tituna domin gudanar da zanga-zanga a jihar Ondo.

Lamarin ya faru ne a yankin Akoko da ke jihar inda mafi yawanci ba su saka sutura a cikinsu ba.

Mata sun fito kan tituna domin gudanar da zanga-zanga
Wasu mata sun fito kan tituna tsirara domin gudanar da zanga-zanga a jihar Ondo. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ondo: Mata sun fito zanga-zanga kan tituna

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnati ta tona shirin dan kasar waje na kawo cikas ga mulkin Tinubu

Matan kamar yadda Daily Trust ta tattaro sun fito ne domin nuna damuwa kan kisan gilla da makiyaya suke yi musu da lalata gonaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wani manomi Sunday Ayeni ya rasa ransa saboda hatsaniya da makiyayi a cikin gona.

An tsinci gawar Ayeni da karen farautansa a karshen mako wanda haka ya tilasta manona kauracewa gonakinsu.

Matan sun bayyana halin da suke ciki

Mai magana da yawun dandazon matan, Abigail Ojo ta zargi makiyaya da cin zarafin mata a gonakinsu.

Ojo ta ce sun kauracewa gonakinsu saboda rashin kwanciyar hankali inda ta ce ba za su koma ba har sai an samu tsaro.

"Ba za mu lamunci irin wannan cin zaraf da rashin tsaro a gonakinmu ba, dole a kawo karshen wannan lamari."

- Abigail Ojo

Ojo ta roki jami'an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wurin tabbatar da sun dakile matsalar tsaro da ta addabe su.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Basaraken gargajiya a yankin, Adebori Adeleye ya ba su tabbacin cewa an dauki mataki kan matsalar tsaro a yankin.

Basarake ya zargi makwabtansu kan kisan al'ummarsa

Kun ji cewa Basarake mai daraja ta daya a jihar Taraba ya fadi musabbabin tashin hankali a yankinsa da ke garin Takum.

Sarkin Takum, Barista Sopiya Ahmadu Gboshi III ya zargin masu kai hare-hare a yankin daga karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.