Tinubu ya Fito da Salon Tsarin Tsaro a Arewa Domin Maganin Ƴan Bindiga
- Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fito da hanyar maganin yan bindiga da suka addabi jihohin Arewacin Najeriya
- Tinubu ya dauki matakin ne biyo bayan yawaitar kai hare hare ga manoma da yan bindiga suke yi a gonakin da sanya musu haraji
- Wani shugaban kungiyar manoma a Najeriya, Kabir Ibrahim ya yi martani kan tsarin da shugaban kasar ya kawowa manoman Arewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Gwamnatin Najeriya ta fito da tsarin sanya jami'an tsaro domin hana yan bindiga kai hari a gonaki.
Sufeton yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun ya bayyana matakin da suka fara dauka a wasu yankunan Arewa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata kungiyar manoma ta mika godiya ga Bola Tinubu kan kawo tsarin a daidai wannan lokacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun addabi manona
Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sun addabi manona a Najeriya ta inda suka kashe kimanin manoma 332.
Haka zalika ƙididdiga ta nuna cewa manoma sun biya yan bindiga harajin kudi da ya haura Naira miliyan 139 a yankin Arewa.
An saka jami'an tsaro a gonaki
Daily Post ta wallafa cewa sufeton yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya tabbatar da cewa jami'an yan sanda sun fara kewayawa zuwa gonaki a Arewa Maso Gabas.
Haka zalika jami'in rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji sun fara sintiri a gonakin Arewa ta Tsakiya da ta Yamma.
Jami'an tsaro sun dauki matakin ne domin samar da cikakkiyar kariya ga manoma a lokacin damina.
Kungiyar manoma ta yi godiya
Wani shugaban kungiyar manoma, Kabir Ibrahim ya ce samun jami'an tsaro a gonaki na karfafa musu gwiwa.
Sai dai duk da haka ya yi kira kan muhimmacin magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya baki daya.
Yan bindiga sun sace manomi a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru Sharehu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da basaraken a lokacin da ya kamo hanyar dawowa gida daga gonarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng