Bayan Fallasar Kawu Sumaila, An gano albashin da Sanatoci Ke Lakumewa Duk Wata

Bayan Fallasar Kawu Sumaila, An gano albashin da Sanatoci Ke Lakumewa Duk Wata

  • Bayanai na ta ƙara samuwa kan albashin da sanatocin Najeriya ke karɓa duk wata wanda ya daɗe ba a sani ba
  • Bincike ya nuna cewa albashin da sanatoci 99 na majalisar ke karɓa yana laƙume N2bn duk wata idan aka yi amfani da N21m da Kawu Sumaila ya ce ana ba shi
  • Wannan adadin na N2bn bai ƙunshi albashin da ake biyan shugabannin majalisar su 10 ba, waɗanda har yanzu ba a san abin da ake biyansu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Alamu sun nuna cewa adadin albashin sanatoci 99 na majalisar dattawan Najeriya duk wata ya haura N2bn.

Ɗaya daga cikinsu Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila (NNPP, Kano), a ranar Laraba ya tabbatar da cewa yana karbar kusan N21m duk wata a matsayin albashi.

Kara karanta wannan

Albashin N21m: Majalisa ta bayyana gaskiya kan abin da ake biyan sanatoci

Albashin sanatoci na kai N2bn duk wata
Albashin sanatocin Najeriya 99 na kai N2bn duk wata Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Albashin sanatoci na laƙume N2bn

Sai dai ya ce bai san adadin kuɗin da shugaban majalisar dattijawa, mataimakin shugaban majalisar da sauran shugabanni takwas na majalisar ke karɓa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan fallasa da Kawu Sumaila ya yi ya nuna cewa duk wata sanatoci 99 da ba shugabanni ba ne a majalisar dattawan, ana biyansu N2.09bn, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Nawa ne albashin shugabannin majalisa?

Har yanzu dai ba a san adadin abin da shugabannin majalisar ke karɓa ba, inda ko a baya sanatoci da dama sun sha faɗin cewa ba su san abin da waɗannan shugabannin ke samu ba duk wata.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, domin sanin haƙiƙanin abin da suke karɓa ya ci tura, domin bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba sannan bai dawo da saƙon da aka tura masa ba domin sanin abin da shugabannin ke karɓa.

Kara karanta wannan

Bayan fadin albashin sanatoci, Kawu Sumaila ya yi sabuwar fallasa

Abin da ake biyan sanatoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kuɗi (RMAFC) ta yi ƙarin haske kan albashin da ƴan majalisar dattawa ke karba a kowanne wata.

Hukumar RMAFC ta ce kowanne sanata daga cikin sanatoci 109 da ke a majalisar dattawa na karɓar albashi da alawus na ₦1,063,860 a duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng