Bayan Tabbatar da Mafi Ƙarancin Albashi, an Lissafa Karin da Ma'aikata Za Su Samu

Bayan Tabbatar da Mafi Ƙarancin Albashi, an Lissafa Karin da Ma'aikata Za Su Samu

  • Hukumar kula da albashi da alawus na Tarayya ta lissafa yadda kananan ma'aikata za su samu albashi
  • NSIWC ta kammala lissafin ne bayan amincewa da karin mafi ƙarancin albashi da Gwamnatin Tarayya ta yi
  • Legit Hausa ta tattauna da masanin tattalin arziki, Aminu Gwadabe inda ya yi sharhi kan lamarin karin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsarin yadda kananan ma'aikatanta za su samu ƙarin albashi.

Gwamnatin ta fitar da tsarin ne bayan amincewa da mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000.

An fitar da adadin yadda ma'aikata za su kwashe bayan karin albashi
Hukumar NSIWC ta lissafa karin albashin kananan ma'aikata. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Za a lissafa karin albashin manyan ma'aikata

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da haka ga jaridar The Nation a jiya Laraba 14 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Abba Kabir ya fusata da zargin APC, ya fadi yadda aka yi game da zargin badakala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce nan ba da jimawa ba za a tura lissafin albashi zuwa ofishin babban mai kula da kudin Gwamnatin Tarayya.

Sai dai majiyar ta ce za a kammala lissafin albashin manyan ma'aikata nan da makwanni biyu zuwa uku masu zuwa.

Karin albashi: Hukumar NSIWC ta yi lissafi

Hukumar kula da albashi da alawus na Tarayya (NSIWC) ita ta lissafa kasafin kudin domin tabbatar da ya daidaita da karin albashin da aka yi.

Kananan ma'aikata su ne ke mataki na daya zuwa biyar sai manyan ma'aikata daga mataki na shida zuwa sama, sai dai abin ya danganta da ma'aikatar.

Ƙananan ma'aikata wadanda su ne abin zai fi shafa kai tsaye za su ga albashinsu ya canza daga akalla N30, 000 zuwa N70, 000.

Tattaunawar Legit Hausa da masanin tattalin arziki

Kara karanta wannan

Ya haura miliyan 20: Sanata Kawu Sumaila ya fadi albashin da ya ke karba duk wata

Legit Hausa ta tattauna da masanin tattalin arziki, Aminu Gwadabe inda ya yi sharhi kan lamarin.

Gwadabe ya ce ana cikin bukata sosai na karin albashi duba da matsin tattalin arziki wanda ya ke kawo cikas.

Ya ce kan tashin farashin kaya daman nema da kuma samuwar abin da ake nema ke jawo ta, game hauhawan farashin kaya sai dai ayi ta hasashe amma ana bukatar ƙarin albashi.

Kan batun yadda hakan zai shafi wadanda ba su aikin gwamnati, Gwadabe ya ce:

"Gaskiya su ne abin dubawa, gwamnati tana ta fitar da tallafi kamar yadda muke gani, muhimmin abu shi ne mutane su sami abin yi."
"Daman abin da ya kamata gwamnatin ta yi ta taimakawa yan kasuwa da inganta asibiti da makarantu saboda su ma su samu sauki ba sai dole sun karbi albashi ba."

- Aminu Gwadabe

Sanatan Kano ya fadi albashinsa a Majalisa

Kun ji cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya bayyana yadda yake daukar albashi da alawus a Majalisar Dattawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Wa'adinka ya kare": Gwamna ya fusata kan ikirarin mai murabus a gwamnatinsa

Sumaila ya bayyana haka yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan makudan kudi da yan Majalisun Tarayya ke dauka a kasar..

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Aminu Gwadabe avatar

Aminu Gwadabe (President at Association of Bureaux de Change Operators of Nigeria) Alhaji Aminu Gwadabe is the president of the Association of Bureau De Change Operators of Nigeria (ABCON) that represents the interests of licensed Bureau de Change operators in Nigeria. Gwadabe comments on issues relating to the foreign exchange market, currency exchange rates, and economic policies in Nigeria over the years.