'Yan Damfara Sun Yi Wa Bankin Najeriya Kutse, Abokan Hulda Sun Shiga Matsala
- Abokan huldan bankin GT sun shiga damuwa bayan yan damfara sun yi nasarar kwace ikon shafin yanar gizon bankin
- Abokan huldan bankin da dama sun yi kokarin ziyartar shafin amma ya ci tura saboda tsautsayin da ya afkawa bankin
- Masana na ganin hakan ka iya faruwa musamman an samu akasi wasu sun samu damar yashe bayanan bankin da amfani da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu da ake zargi 'yan damfara ne sun yi kutse a yanar gizon bankin Guarantee Trust a Najeriya.
Lamarin ya faru ne a yau Laraba 14 ga watan Agustan 2024 wanda ya yi sanadin dakile abokan huldarsu wurin amfani da bankin.
'Yan damfara sun yi kutse a Bankin GTB
Daily Trust ta tattaro cewa abokan huldan bankin sun yi bakin kokarinsu domin ziyartar shafin bankin amma ya ki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu ziyartar shafin yanar gizo na bankin kamar haka www.gtbank.com sun yi ta kokarin shiga da daren yau misalin karfe 10:30 amma ya ki ba da dama.
Rahotannin sun tabbatar da cewa hakan na zuwa ne bayan sabunta adireshin na tsawon shekaru biyar daga 2024 zuwa 2029.
Yadda wasu ke kutse a bankunan Najeriya
Wani masani a harkar yanar gizo ta bangaren bankuna ya ce watakila an samu akasi wurin sace bayanan sirrin bankin.
Ya ce ana iya samun irin haka musamman wasu dillalai na iya sacewa tare da siyarwa kan farashi mai tsadan gaske.
Bankin ya yi magana kan lamarin
Bankin ya fitar da sanarwar kan labarin cewa yan damfara sun yi kutse tare da kwashe bayanan abokan hulda.
Ya ce tabbas an yi kokarin kutse amma bayanan abokan huldarsu babu abin da ya same su.
Bankin ya ce bai ajiye bayanan abokan hulda a yanar gizo inda ya tabbatar musu cewa bayanansu na cikin aminci.
'Yan damfara sun yi kutse a bankuna
Kun ji cewa kusan Naira Biliyan 1 ne aka yi asararsu ta dalilin zamba da sata ta hanyoyin biyan kudi da mu'amalar yau da kullum a cikin farkon 2023.
Hakan ya biyo bayan fargabar da Hukumar Inshorar Ajiyar Kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana kan yawaitar satar da ake samu a bankuna.
An bayyana hakan ne a cikin wani rahoto mai suna "Rahotanni kan zamba da sata a bankunan Najeriya", da cibiyar horar da harkokin kudi (FITC) ta buga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng