Wani Basarake a Arewa Ya Zargi Makwabciyar Jiharsu da Hallaka Masa Al'umma

Wani Basarake a Arewa Ya Zargi Makwabciyar Jiharsu da Hallaka Masa Al'umma

  • Mai sarautar gargajiya a Takum da ke jihar Taraba, Sopiya Ahmadu Gboshi ya nuna damuwa kan rasa rayuwa a yankin
  • Basaraken ya zargi yan yankin karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue da ba da gudunmawa wajen rashin tsaro
  • Wannan na zuwa ne bayan kisan wasu fasinjoji shida da yan bindiga suka yi a kan hanyar Takum zuwa Wukari a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Basarake mai daraja ta daya a jihar Taraba ya fadi musabbabin tashin hankali a yankinsa.

Sarkin Takum, Barista Sopiya Ahmadu Gboshi III ya zargin masu kai hare-hare a yankin daga karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun wargaza kotu a Kano, sun jawo asarar N1bn yayin zanga zanga

Basarake ya soki makwabtansu da kisan kiyashi kan alummarsa
Sarkin Takum, Barista Sopiya Ahmadu ya zargi wasu daga Benue kan rashin tsaro. Hoto: Sopiya Ahmadu Gboshi III.
Asali: Facebook

Taraba: Basarake ya zargi makwabtansu kan tsaro

Basaraken ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar a yau Laraba 14 ga watan Agustan 2024, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya bukaci karin hakuri daga al'ummar yankin yayin da suke fama da hare-haren yan bindiga.

"Mafi yawan masu aikata laifuffukan suna fitowa ne daga karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue."
"Jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki suna iya bakin kokari domin ganin an zakulo wadanda suke aikata laifuffukan."

- Sopiya Ahmadu Gboshi

Basarake ya yabawa gwamnan Taraba kan kokarinsa

Basaraken daga bisani ya yabawa Gwamna Agbu Kefas wurin daukar matakai masu inganci domin dakile matsalar tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun hallaka fasinjoji shida a kan hanyar Takum zuwa Wukari a jihar.

Yan bindigan sun farmaki mutanen ne a tsakanin garin Chanchangi na ƙaramar hukumar Takum da ƙauyen Saa’yi a jihar Benue.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun sace takardun shari’ar Ganduje a kotu lokacin zanga zanga a Kano

Yan bindiga sun hallaka basarake a Taraba

Kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka basaraken kauyen Chanchangi da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba, Kumbiya Tanimu da ɗansa.

Maharan sun yi kwantan ɓauna tare ɗa hallaka basaraken da ɗansa a kan titin Takum-Chanchangi a lokacin da suke hanyar dawowa daga jana'iza.

Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya umarci jami’an tsaro da kamo makasan tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.