Dattijon Arewa Ya Jaddadawa Tinubu Matsayarsa, Yakasai Ya Fadi Matsalar Najeriya

Dattijon Arewa Ya Jaddadawa Tinubu Matsayarsa, Yakasai Ya Fadi Matsalar Najeriya

  • Daya daga cikin jija-jigan Arewacin kasar nan, Tanko Yakasai Ya yi martani da masu bukatar a sauya kundin mulki
  • Dattijon kasar, Alhaji Yakasai ya musanta cewa kundin tsarin mulkin ne abin da ke jawo cikas wajen gudanar da al'amura
  • Ya fallasa wadanda su ke kawo cikas a kasar nan, inda ya zargi masu gudanar da mulki Najeriya da hana ruwa gudu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dattijon kasa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa ba kundin tsarin mulkin Najeriya ce ke da matsala ba, kar a bar jaki ana dukan taiki.

Alhaji Yakasai, wanda shi ne uban kungiyar Arewa ta ACF ya shaida haka ne ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Tanko
Jigon ACF ya ce tunanin shugabannin kasar nan ne matsalarta Hoto: Salihu Tanko Yakasai/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Cable ta tattaro cewa dattijon ya bayyanawa shugaban kasa hanyoyin da ya dace abi wajen inganta kasar nan baki dayanta, a maimakon sauya kundin tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana damuwa a kan yadda wasu 'yan kungiyar kishin kasa ta The Patriots ta shaidawa shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa kundin tsarin mulki ne matsalar.

Su wanene matsalar Najeriya?

Jaridar Daily Post ta tattaro cewa dattijon ya ce jagororin kasar nan ne su ke hana ta ci gaba.

Ya bayyana cewa idan ba a sauya tunanin jagororin kasar nan ba, babu irin kundin tsarin mulkin da zai yi tasiri wajen bunkasa Najeriya

Dattijon ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya yi shawara da wasu daban, kar ya yi gaggawar daukar shawarar da kungiyar The Patriots ta ba shi.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Arewacin Najeriya, mata da miji da 'ya'yansu 5 sun mutu bayan cin rogo

Za a sauya kundin mulkin Najeriya

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya na shirye-shiryen yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan gyaran fuska ta hanyar mayar da ita tsarin mulkin shiyya.

Dan majalisa, Hon. Akin Fabohunda da ya gabatar da kudirin dokar ya bayar da tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin shugaba Tinubu ya karbi kudirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.