Hukumar EFCC Ta Kawo Shawarar Yadda Za a Cafke Barayin Man Fetur

Hukumar EFCC Ta Kawo Shawarar Yadda Za a Cafke Barayin Man Fetur

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta mika bukatar yadda ta ke son a rika shari'a da masu sata a bangaren fetur
  • Daraktan bincike na hukumar, Abdulkarim Chukkol ya bayyana cewa su na bukatar gwamnati ta kafa kotu na musamman
  • Chukkol ya bayyanawa kwamitin binciken sata a bangaren fetur na majalisa cewa aikin kotun zai zama kan satar fetur kadai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta nemi gwamnatin tarayya ta samar da kotuna na musamman saboda barayin fetur.

Daraktan bincike na hukumar EFCC, AbdulKarim Chukkol ne ya shaida bukatarsu ga kwamitin binciken badakalolin sashen fetur na majalisar ƙasa a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Hukumar NNPCL
Hukumar NNPCL na son a samar da kotun hukunta barayin fetur Hoto: NNPCL Limited
Asali: Facebook

Channels Television ta tattaro cewa darakta Chukkol ya ce yanzu haka ana binciken zarge-zarge a sashen guda 400 a shekarar 2019, yayin da aka hukunta mutane 200 a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Chukkol na ganin samar da kotun zai saukaka aikin EFCC na bibiyar masu sace dukiyar yan kasa a bangaren fetur.

"Bangaren shari'a na da muhimmanci," EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana muhimmancin da bangaren shari'a ke da shi wajen yakar yi wa kasar nan ta'annati, Leadership ta wallafa.

A watan Yuni ne shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya bayyana haka, inda ya nemi a samar da kotuna na musamman, wanda aikinsu kawai shi ne hukunta barayin fetur.

Mele Kyari ya bayyana cewa masu lalata kayan da ke bangaren fetur na taka muhimmiyar rawa wajen dakile nasarorin da ake samun a sashen.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Kotu ta ba EFCC umarnin rufe miliyoyin daloli a asusun ƴan Kirifto

EFCC za ta rufe asusun 'yan kirifto

A baya kun ji yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu amincewar samar da kotun tarayya wajen rufe asusun 'yan kirifto guda hudu.

Hukumar EFCC za ta rufe asusun da kudin cikinsu ya kai Dala Miliyan 37 bisa zargin suna da hannu a cikin daukar nauyin ta'addanci da zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.