Makarantun Jihohi 22 da NELFund Ta Kara Tantancewa a Ba Dalibai Aron Kudin Karatu

Makarantun Jihohi 22 da NELFund Ta Kara Tantancewa a Ba Dalibai Aron Kudin Karatu

  • Asusun ba da lamunin karatu na Najeriya NELFund ya kara tantance wasu makarantu da dalibansu za su ci gajiyar bashi
  • Idan ba a manta ba, Bola Tinubu ya kaddamar da shirin ba da lamunin karatu domin daliban Najeriya su yi karatu mai zurfi
  • A wata sanarwa da asusun ya fitar yau, ya ce daliban manyan makarantun 22 da yanzu aka tantance za su iya neman rancen kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Asusun ba da lamunin karatu na Najeriya NELFund ya ce ya tantance karin wasu manyan makarantu 22 mallakar jihohi domin ba dalibansu rancen kudi.

Aiwatar da shirin ba da lamuni ga daliban manyan makarantun kasar nan na shi ne babban shirin Shugaban Bola Tinubu a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

NELFund ya tantance karin manyan makarantu 22 mallakin jihohi
NELFund: Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kirkiro shirin ba da lamunin karatu. Hoto: Frédéric Soltan/Getty Images, @officialABAT/X
Asali: UGC

NELFund ya tantance karin makarantu

An sanar da tantance karin jami'o'in ne a cikin wata sanarwa wacce aka wallafa a shafin @NELFUND na X a ranar Laraba, 14 ga Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Asusun ba da lamunin karatu na Najeriya na sanar da jama'a cewa dalibai daga wadannan manyan makarantu 22 na gwamnatin jihohi za su iya neman lamuni a shafin: nelf.gov.ng
“Wannan ya biyo bayan nazarin da kwamitin da ke da alhakin tsarin tantance dalibai ya yi kan makarantun.
Tun da fari, an tantance manyan makarantu 86 mallakar jihohi, wanda ya kawo jimillar manyan makarantun zuwa 108 kuma dalibansu na iya neman rancen kudin yanzu."

NELFund: Sunayen makarantun da aka tantance

1. Jami'ar jihar Abia, Uturu

2. Kwalejin ilimi ta Nsugbe

3. Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Anambra

4. Jami'ar jihar Delta, Abraka.

Kara karanta wannan

Matatar man Dangote za ta sayar da litar fetur a kan N600? Kamfanin ya yi karin haske

5. Kwalejin fasaha da koyon ayyuka ta jihar Delta, Otefe-Oghara

6. Jami'ar jihar Ekiti, Isan-Ekiti

7. Jami'ar jihar Kogi, Kabba.

8. Jami'ar Prince Abubakar Audu, jihar Kogi.

9. Jami'ar jihar, Kwara

10. Kwalejin fasahar kiwon lafiya ta jihar Kwara

11. Jami'ar Abdulkadir Kure, Minna

12. Kwalejin fasa da kiwon lafita ta jihar Ogun, Ilese-Ijebu

13. Kwalejin fasaha da koyon ayyuka Moshod Abiola

14. Jami'ar ilimi ta Emmanuel Alayande, Oyo

15. Kwalejin fasaha da koyon ayyuka ta Ibadan

16. Kwalejin fasaha da koyon ayyuka ta Oke Ogun, Saki

17. Jami'ar jihar Rivers, Port Harcourt

18. Kwalejin fasaha da koyon ayyuka ta Kenule Beeson Saro-Wiwa

19. Kwalejin koyon jinya da ungozoma ta Shehu Sule, Damaturu

20. Kwalejin koyon mulki, gudanarwa da fasaha ta Potiskum, jihar Yobe.

21. Kwalejin noma, kiminiya da fasaha ta Gujba

22. Kwalejin ilimi kan harkokin shari'a ta Nguru

NELFund :alibai sun karbi alawus

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya farin ciki a fuskar daliban jami'a, N20000 ta shiga asusun dalibai 20371

A wani labarin, mun ruwaito cewa daliban manyan makarantun da suka samu shiga cikin shirin ba da lamunin karatu na NELFund sun karbi alawus na N20,000 na watan Yuli.

A zantawar da aka yi da wasu dalibai, sun nuna farin cikinsu da samun kudin, inda mafi yawansu suka ce sun sayi kayan abinci tare da biyan wasu bukatu na rayuwar makarantarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.