An Kama Wasu Ƴan Siyasa da Suka Ba Masu Zanga Zanga N4bn a Abuja da Jihohin Arewa 3
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu ya ce an kama wasu ƴan siyasa da suka bada kuɗaɗe a zanga-zanga
- NSA ya bayyana cewa gwamnati ta kama ƴan siyasar ne a Abuja da wasu jihohi uku bisa zargin ɗaukar nauyin zanga-zangar yunwa
- Nuhu Rubadu ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wurin taron majalisar magabata karƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta kama wasu ƴan siyasa da suka ba da gudummuwar maƙudan kuɗi a zanga-zangar da aka yi kwanan nan a Najeriya.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka a taron majalisar magabata da aka yi ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024.
Punch ta tattaro cewa Nuhu Ribadu ya gabatar da rahoto mai taken, "yadda zanga-zanga ta gaba tsaron ƙasa," a taron wanda ya samu halartar tsoffin shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƴan siyasar da aka kama, ana zargin suna daga cikin manya-manyan masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da aka gudanar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da Muhammadu Buhari da Dokta Goodluck Ebele Jonathan, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Jihohin da aka kama ƴan siyasa
A cewar majiyoyin, an kama su ne a Abuja, Kano, Kaduna da Katsina duk a Arewacin Najeriya.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce:
"Sun kuma gano cewa wasu ’yan siyasa sun ba da N4bn don gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa."
Har ila yau gwamnatin Bola Tinubu ta ƙwace kudi N84bn da aka turo daga ƙasashen ƙetare domin ruwa wutar zanga-zanga.
Jerin tallafi 11 na gwamnatin tarayya
A wani rahoton kuma kun ji cewa ’yan Najeriya na da damar neman akalla tallafi 11 da gwamnatin tarayya ta kirkiro domin saukakawa al'ummar kasar.
Waɗannan manyan shirye shiryen sun shafi fannoni kamar ilimi, sufuri, kasuwanci, gidaje da sana'o'in dogaro da kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng