Tutar Rasha: Gwamnati ta Tona Shirin Dan Kasar Waje na Kawo Cikas ga Mulkin Tinubu

Tutar Rasha: Gwamnati ta Tona Shirin Dan Kasar Waje na Kawo Cikas ga Mulkin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan wasu abubuwa da suka faru a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya
  • Nuhu Ribadu ya yi bayani kan wanda ake zargi da amfani da raba tutocin kasar Rasha a wasu jihohi a Arewacin Najeriya
  • Haka zalika gwamnatin tarayya ta bayyana makudan kudi da ta kama da ake shirin shigo da su Najeriya ga masu zanga zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan wasu abubuwan da suka faru a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Gwamnatin tarayya ta yi bayani ne a zaman majalisar magabata na kasa da ta gudana a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi abin da Tinubu ya tattauna da Buhari, shugabanni a taron magabata

Nuhu Ribadu
Gwamnati ta gano wanda ya raba tutar Rasha a Najeriya. Hoto: @AjuriNgalele
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya yi magana kan masu daga tutar Rasha a lokacin zanga zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu daga tutar Rasha a Najeriya

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa suna zargin wani dan kasar waje da daukan nauyin raba tutocin Rasha a lokacin zanga zanga domin kawo matsala ga mulkin Tinubu.

Har ila yau, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa yan sanda suna daf da wallafa sunan mutumin cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Rundunar yan sanda ta cafke mutane da dama musamman a jihohin Kano da Kaduna da zargin yin zagon kasa ga Najeriya kan amfani da tutar Rasha.

Gwamnati kama kudin yan zanga zanga

Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta kwace kudi N83bn da aka turo ga yan zanga zanga a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta gano kudin Kirifto da ya kai $50m da aka turo ta asusun banki guda hudu ga masu zanga zangar.

Haka zalika gwamnatin ta kara da cewa ta gano kudi N4bn da aka turo ga masu zanga zanga a jihohin Kano, Katsina, Kaduna da birnin tarayya Abuja.

Tinubu ya kafa doka ga likitoci

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya kawo dokar da za ta canza tsarin da ya ba likitocin Najeriya damar fita zuwa kasashen waje sakaka.

Gwamnatin tarayya ta ce an kawo dokar ne domin inganta lafiyar yan kasa wajen samar da wadatattun ma'aikatan lafiya a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng