Zo Ka Nema: Jerin Tallafi 11 na Gwamnatin Tarayya da Shafukan da Ake Rijistarsu

Zo Ka Nema: Jerin Tallafi 11 na Gwamnatin Tarayya da Shafukan da Ake Rijistarsu

  • ’Yan Najeriya na da damar neman akalla tallafi 11 da gwamnatin tarayya ta kirkiro domin saukakawa al'ummar kasar
  • Waɗannan manyan shirye shiryen sun shafi fannoni kamar ilimi, sufuri, kasuwanci, gidaje da sana'o'in dogaro da kai
  • Mai tallafawa shugaban kasa kan harkokin sadarwar zamani, Olusegun Dada, ya zayyana shirye shiryen da shafukansu na intanet

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da fitar da wasu shirye shirye na tallafawa ‘yan Najeriya daga bangarori daban-daban na rayuwa.

Kimanin shirye shiryen ba da tallafi 11 ne gwamnatin tarayyar ta kaddamar tare da shafukansu na yanar gizo inda 'yan Najeriya za su iya neman tallafin.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Shafukan yanar gizo da 'yan Najeriya za su nemi tallafi daga gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirye shiryen tallafi 11, da shafukan da ake nema. Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Tinubu kan harkokin sadarwar zamani, Olusegun Dada, ya wallaga shriye-shiryen 11 da shafukansu na intanet a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan shirye-shiryen sun shafi sassa daban-daban na rayuwar al'umma da suka hada da lamunin karatu, gidaje, da tallafin kasuwanci da sauransu.

Shirye shiryen tallafi 11 da shafukansu

A kasa, mun zayyano shirye-shiryen tallafi 11 da 'yan Najeriya za su iya nema da kuma shafukan da za su shiga domin yin rijista

1. Shirin ba da lamunin karatu

http://nelf.gov.ng

2. Shirin ba da tallafi na iskar gas din CNG

https://pci.gov.ng

3. Shirin ba da rancen kudi ga 'yan kasuwa (CCC)

https://credicorp.ng

4. Shirin ba ta tallafi na kirkira da fasahar zamani (iDiCE)

https://boi.ng/iDiCE

5. Shin ba da tallafi ga masu sana'o'in hannu (SUPA)

https://SUPA.itf.gov.ng

Kara karanta wannan

Bayan gama zanga zanga, gwamna a Arewa ya ɗauko hanyar share hawayen talakawa

6. Shirin ba matasa lamuni karkashin NIYA

https://NIYA.ng

7. Shirin ba da tallafi ga matasa masu fikira (NATEP)

http://natep.gov.ng

8. Shirin ba da rancen kudi da matsakaita da kananun 'yan kasuwa

https://boi.ng/micro-business

9. Shirin ba da lamunin mallakar gida

http://fha.gov.ng/ongoing-projects

10. Shirin ba da horo da biyan aiki na NDDC

https://nyis.nddc.gov.ng

11. Shirin ba da tallafin kasuwanci na TUCN

https://tucnigeria.org.ng

Shirin mallakar gida na 'Renewed Hope'

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin mallakar gidaje ga 'yan Najeriya na 'Renewed Hope' da nufin magance matsalar karancin gidaje.

Mun tattaro hanyoyi biyar da za a bi domin yin rijista, neman gida, duba bayanin gida, tsarin biyan kudi da ma hanyoyin biyan kudin domin mallakar gida a shirin 'Renewed Hope.'

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.