Gwamna Ya Fada Hannun Ƴan Damfara, Ana Tura Sakon Neman Kudi a Lambarsa ta WhatsApp

Gwamna Ya Fada Hannun Ƴan Damfara, Ana Tura Sakon Neman Kudi a Lambarsa ta WhatsApp

  • ‘Yan damfara sun yi kutse a lambar WhatsApp din gwamnan Akwa, Ibom Umo Eno, inda suka aika da sakonnin zamba ga abokan huldarsa
  • Sakataren yada labaran Gwamnan, Ekerete Udoh, ya nuna cewa ‘yan damfarar sun yi wa lambar WhatsApp din kutse da nufin damfarar mutane
  • An yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani sako na neman kudi, yayin da aka fara bin diddigin wadanda suka yi wannan aika-aika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom - Rahotanni sun bayyana cewa 'yan damfarar yanar gizo da ake kira da 'Yan Yahoo sun yi kutse a lambar WhatsApp din Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom.

An ruwaito cewa 'yan damfarar har sun fara tura sakonni ga wasu daga cikin mutanen da gwamnan ke mu'amala da su a dandalin na WhatsApp.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Gwamnatin Akwa Ibom ta yi karin haske yayin da 'yan damfara suka yiwa gwamna kutse
Yan damfara sun yiwa lambar gwamnan Akwa Ibom kutse, suna aika sako a WhatsApp. Hoto: @aksgovt/X, Picture alliance/Getty Images
Asali: UGC

'Yan damfara sun yiwa gwamna kutse

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a ranar Talata, 'yan dambarar sun tura sakon neman rancen kudi ga mutanen, da alkawarin cewa za a mayar masu da kudin daga baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, Ekerete Udoh, babban sakataren watsa labaran Gwamna Umo ya ce 'yan damfara ne ke kokarin yaudarar mutane ba gwamnan ba.

Sanarwar Ekerete Udoh ta nuna cewa gwamnatin jihar ta kai lamarin ga hukumomin da abin ya shafa, kuma nan ba da wani lokaci ba za a magance matsalar.

"Ka da a damfare ku" - Gwamnati ga jama'a

Jaridar New Telegraph ta ruwaito sanarwar gwamnatin jihar ta ce:

"Mun samu rahoton cewa wasu 'yan damfara sun fara tura sakon neman kudi daga wajen mutane bayan da suka yi kutse a lambar WhatsAppp din gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

"Muna gargadin mutane cewa duk wani sako da aka tura na neman kudi da sunan gwamnan to yaudara ce, don haka mutane su guji wata mu'amala da wannan lambar.
"Tuni aka kai wannan lamarin ga hukumomin da abin ya shafa, kuma nan ba da jimawa ba za a kama tare da hukunta wadanda suka yi wannan danyen aikin."

Osun: An yi wa lambar gwamna kutse

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa wasu miyagu sun yi wa daya daga cikin lambobin wayar gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke kutse.

Mai magana da yawun gwamnan, Mallam Olawale Rasheed, wanda ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar, ya bukaci jama’a da su yi watsi da kira ko sakwanni daga lambar gwamnan: +2348033657555.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.