Matatar Man Dangote Za Ta Sayar da Litar Fetur a kan N600? Kamfanin Ya Yi Karin Haske

Matatar Man Dangote Za Ta Sayar da Litar Fetur a kan N600? Kamfanin Ya Yi Karin Haske

  • Kamfanin Dangote ya yi magana kan rahotannin da ke yawo a kafofin yada labarai cewa matatar mai ta kayyade farashin fetur
  • Kamfanin na magana ne kan wani rahoto da ya nuna cewa 'yan kasuwa sun yi hasashen fetur din Dangote zai fita kasuwa kan N600
  • A sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne domin babu inda ya ce ya kayyade farashin litar fetur zuwa N600

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya, kuma na biyu a Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ce bai kayyade farashin da matatar mansa za ta sayar da fetur ba.

Aliko Dangote ya ce rahotannin da ake yadawa a kafofin yada labarai cewa matatar za ta sayar da litar fetur dinta a kan N600 ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

A karo na 6, NNPCL ya karya alkawarin da ya dauka a kan gyara matatar Ribas

Kamfanin Dangote ya yi magana kan kayyade farashin man fetur.
Kamfanin Dangote ya ce bai kayyade farashin litar fetur zuwa N600 ba. Hoto: Dangote Group
Asali: Facebook

Dangote ya magantu kan ikirarin IPMAN

Anthony Chiejina, shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana hakan a wata sanarwa a shafin kamfanin na X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"An ja hankalinmu kan wani labari da jaridar Punch ta wallafa a ranar Talata, 13 ga watan Agusta mai taken 'Yan kasuwa sun yi hasashen Dangote zai sayar da litar fetur kan N600.
"Muna so mu sanar da al'umma cewa kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN) ba su kai ga zama abokan huldarmu ba har yanzu."

Farashin fetur daga Dangote zai fita a N600?

Anthony Chiejina ya kara da cewa ko sau daya kamfanin Dangote bai taba tattaunawa da kungiyar IPMAN kan farashin man fetur ba.

"Ku kungiyar IPMAN ba ta da wani hurumi ko iko na yin magana a madadinmu, walau maganar da za ta amfane mu ko kuma akasin hakan.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

"Muna kira ga jama'a da su kauracewa irin wannan kanzon kuregen. Mu na da kafofin da muke fitar da sanarwa ga abokanan huldarmu da sauran masu ruwa da tsaki."

Dangote: Farashin dizal ya karye zuwa N1,225

A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin litar AGO wanda aka fi sani da dizal ya fadi daga N1,700 sabanin N1,350 da aka saba sayensa a baya.

An ce wannan ragin da aka samu na kusan N350 a cikin 'yan makonni ya faru ne sakamakon fara sayar da dizal din da matatar man Dangote ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.