An Shiga Jimami Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Basarake a Jihar Arewa

An Shiga Jimami Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Basarake a Jihar Arewa

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka wani basaraken gargajiya a ƙaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi
  • Ƴan bindigan sun hallaka Onu na garin Itama, Shagari Ebije'ego Job, bayan sun shiga har cikin gidansa yayin harin
  • Marigayin wanda ƴan bindigan suka hallaka ranar Litinin da daddare, shi ne basarake mai ƙarancin shekaru a Dekina

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Ƴan bindiga sun kashe wani basaraken gargajiya, Onu na garin Itama da ke ƙaramar hukumar Dekina a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun hallaka mai martaba, Shagari Ebije’ego Job, a gidansa da ke garin.

'Yan bindiga sun hallaka basarake a Kogi
'Yan bindiga sun hallaka basarake a wani hari a Kogi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka hallaka basaraken

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun bi sawun basaraken har zuwa gidansa sannan suka harbe shi nan take a daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gano babban wanda ake zargi da tsara 'rusa' Najeriya lokacin zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin da ƴan bindigan suka kashe shi ne basaraken gargajiya mafi ƙarancin shekaru a ƙaramar hukumar ta Dekina.

Su wanene su ka kashe basaraken?

Wani mazaunin garin mai suna Adukwu Ajibili ya bayyana cewa ƴan bindigan da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun shiga cikin garin sannan suka nufi gidan basaraken kai tsaye.

"Mun hango ƴan bindigan ɗauke da makamai lokacin da suke tafiya zuwa gidan basaraken da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Litinin."
"Jim kaɗan sai muka fara jiyo ƙarar harbin bindiga daga wajen, wanda hakan ya sanya mutane suka gudu domin tsira da rayukansu."
"Wasu daga cikinmu sun fito bayan ƴan bindigan sun tafi inda muka fahimci cewa an hallaka mai martaba a yayin harin."

- Adukwu Ajibili

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

Kakakin ƴan sandan bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Karfen Sarki cikin ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar tsaron jihar mutum biyar da wasu manoma mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng