Matasa Miliyan 1 Za Su Yi Tattakin Goyon Bayan Tinubu bayan Zanga Zangar Adawa

Matasa Miliyan 1 Za Su Yi Tattakin Goyon Bayan Tinubu bayan Zanga Zangar Adawa

  • Wasu matasa a kasar na sun bayyana goyon bayansu kan kamun mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Wannan na zuwa bayan wasu 'yan kasa sun fusata da halin matsin da ake zargin manufofin Tinubu ne su ka jawo kan talakawa
  • Matasan APC a jihar Ribas sun shirya gudanar da tattalin mutane miliyan 1 domin jaddada goyon bayan salon mulkin Bola Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Matasan APC sun ga rashin dacewar zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kwanaki 10

Tsigaggen shugaban APC na reshen Ribas, Tony Okocha ya ce zanga-zangar ta sauya daga ta lumana zuwa tashin hankali da tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan

Ana sa ran Buhari ya koma Aso Rock, Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa

Tinubu
Matasa za su tattakin goyon bayan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Okocha ya bayyana ra'ayinsa ne bayan jagorantar tattakin matasa masu goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano masu tattakin dauke da kwalaye da rubutun da ke nuna goyon baya ga shugaban kasa, kuma tattakin ya jawo cunkoson ababen hawa na wani lokaci.

"Za mu tsaftace zanga-zanga," Okocha

Tsohon shugaban APC a Ribas, Tony Okocha ya bayyana manufar tattakin mutum miliyan daya da su ke shirin gudanarwa a jihar da cewa za a tsaftace zanga-zanga.

Yan kasar na sun nuna fushinsu a kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin kasar nan, wanda ya jefa su cikin matsi, Channels TV ya wallafa.

Okocha ya yi shagube ga gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ya yi wa masu zanga-zanga tayin kudin burodi maimakon duba hanyar kawo masalaha.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun aiki gwamna da sako zuwa ga Tinubu, sun zayyana bukatunsu

Kotu ta yanke hukunci kan masu zanga-zanga

A baya kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi nasara a kan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin tarayya bayan an tsawaita umarnin hana su taruwa a babban filin wasan Abuja.

A zaman kotun na ranar Talata, Mai shari'a Sylvanus Oriji ya tsawaita wa'adin haramta taron zanga zanga a babban filin wasa na MKO Abiola zuwa 13 Agusta 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.