Yan Ta'adda Sun Tsare Babbar Hanya a Zamfara, An Kwashe Dimbin Matafiya

Yan Ta'adda Sun Tsare Babbar Hanya a Zamfara, An Kwashe Dimbin Matafiya

  • 'Yan ta'adda sun rufe wata babbar hanya a Zamfara, inda su ka kwashe fasinjoji daga cikin motoci guda uku da su ka tare a hanyar
  • Matafiyan na kan hanyar Gusau-Funtua inda su ka yi kicibis da 'yan ta'addan da su ka addabi hanyar tun bayan da damuna ta fada
  • Rundunar 'yan sandan reshen jihar Zamfara ta tabbatar da harin miyagun, inda ta ce an aika sojoji domin fatattakar 'yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Matafiya sun yi kicibis mugun gamo da 'yan ta'adda hanyar Gusau-Funtua a Zamfara, inda miyagu su ka ɗauke fasinjojin mota uku.

Kara karanta wannan

"Ko mutum 1 ba a kashe a lokacin zanga zanga ba," Inji rundunar 'yan sandan Kano

Miyagun dauke da mugayen makamai sun tare motocin a kauyen Margazu da ke karamar hukumar Tsafe, wanda a nan ne su ka tafka ta'asar.

Dauda Lawal
Yan ta'adda sun sace matafiya a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun kuma tare hanyar Unguwan Chida, tare da sace matafiya daga cikin motoci biyar da ke bin hanyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankin sun ce duk da kashe 'yan ta'addan, su na karfin hali wajen cigaba da matsawa masu bin hanyar tun bayan da damuna ta yi karfi.

Harin ta'addanci: Sojoji sun kai dauki

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da harin da 'yan ta'adda su ka kai kan matafiya a hanyar Gusau-Funtua da Unguwar Chida a jihar, Daily Post ta wallafa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Yazid Abubakar ya ce tuni hukumomi su ka tura sojoji domin korar 'yan ta'addan tare da dakile ayyukansu.

Kara karanta wannan

Direban adaidaita sahu ya maida jakar kudin da ya tsinta, yan sanda sun sa cigiya

Bayan isar sojojin wurin ne aka fafata, an samu nasarar ceto wasu daga cikin fasinjojin da aka yi yunkurin sacewa, yayin da miyagun su ka yi daji da sauran.

Yan ta'addan sun kashe sojoji

A baya mun ruwaito cewa an tafka gagarumar asarar rayuka bayan wasu 'tan ta'adda sun yiwa sojoji kwantan bauna tare da kashe sojoji biyu da kona motocin sintiri.

Mummunan lamarin ya afku a jihar Sokoto, amma rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da kakkausar martani kan 'yan ta'addan, tare da kashe miyagu da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.