'Yan Ta'adda 44 Sun Ji Wuta, Sun Miƙa Wuya Yayin da Sojoji Suka Hallaka Wasu a Arewa
- Sojoji sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda biyar a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, sun kwato manyan makamai
- Rundunar ta bayyana cewa sakamakon luguden wutar da sojojin ke yi, mayaƙan Boko Haram 44 da iyalansu sun miƙa wuya
- Sanarwar ta kara da cewa daga cikin makaman da aka kwato har da bama-bamai, bindigu, alburusai da kuma babura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe ƴan ta'adda biyar a yankin ƙaramar hukumar Bama da ke jihar Borno a Arewa maso Gabas.
Bugu da ƙari, bayan tura ƴan ta'addan lahira, dakarun sojojin sun ƙwato bama-bamai, bindigun roka, babura shida da wasu kayan aiki da dama.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin kasa ta Najeriya ta fitar ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, kamar yadda Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce 'yan ta'addan Boko Haram 44 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin da aka tura kananan hukumomin Bama, Dikwa, da Gwoza na jihar Borno.
Sojoji sun kai samame sansanin ISWAP
Sanarwar ta ce:
"A ranar 12 ga Agusta, 2024, sojoji sun kai samame wani sansani da mayaƙan kungiyar ISWAP ke samun mafaka a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
"A samamen sojoji sun kashe ‘yan ta’adda biyar tare da kwato bama-bamai guda biyu, bindigogin roka biyu, Dane guda biyu, bom na RPG daya, AK-47 daya, harsashi 23, babura shida da magunguna iri-iri."
Boko Haram: Ƴan ta'adda sun mika wuya
Rundunar sojojin ta kara da cewa sakamakon luguden wutan da dakaru ke ci gaba da yi kan mayaƙan Boko Haram, ƴan ta'adda 44 sun miƙa wuya tare da iyalansu.
"'Yan ta'addan Boko Haram 44 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin da aka tura a kananan hukumomin Bama, Dikwa da Gwoza a jihar Borno," in ji sanarwar.
Yan China sun faɗa hannun masu garkuwa
A wani labarin kuma ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan ƙasar China biyu da suka shigo Najeriya domin yin aiki a jihar Ogun.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola ta ce jami'an haɗin guiwa na neman ceto su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng