Yankunan Arewa Sun Tsunduma Cikin Duhu Bayan Tirela ta Murtuke Turken Wuta a Kano
- Kamfanin rarraba wuta na kasa (TCN) ya bayyana halin da aka shiga a yankunan Arewa bayan faduwar turken wuta a Gezawa
- TCN ya ce an samu katsewar lantarki a sassan wasu jihohi a yankin Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabashin Najeriya
- Kamfanin ya bayyana babban dalilin katsewar wutar da kuma kokarin da yake wajen ganin lamura sun daidaita cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - An samu katsewar wutar lantarki a wasu sassan jihohin Jigawa da Yobe a Arewacin Najeriya.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa ya bayyana yadda haɗarin mota ya jefa yankunan cikin duhu.
Legit ta tatttaro bayanan da kamfanin TCN ya yi ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Katsewar wutar lantarki a yankunan Arewa
Kamfanin TCN ya bayyana cewa wata babbar mota ce ta tumbuke turken wuta wanda hakan ya jefa al'umma cikin duhu.
TCN ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen Gundumawa a karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.
Yankunan da aka shiga duhu a Arewa
Rahoton Channels Television ya nuna cewa TCN ya bayyana cewa katsewar wutar lantarkin ya shafi kananan hukumomin Machina da Nguru a jihar Yobe.
Lamarin ya shafi ƙananan hukumomin Kaugama, Hadeja, Gumel, Gagarawa, Malammadori, Birniwa, Kafin Hausa, Auyo, Guri, Garki, Taura, Babura, Kirikasamma da Mai Gatari a jihar Jigawa.
Kokarin TCN na dawo da wuta a jihohi
Kamfanin TCN ya bayyana cewa tuni ya dukufa wajen ganin ya samar da sabon turken wuta a kan lokaci.
A yanzu haka dai kananan hukumomin su 17 za su cigaba da zama a cikin duhu har zuwa lokacin da za a kammala gyare-gyaren.
An sace randar wutar lantarki a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Gombe karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta dauki mataki kan kansila da dagaci bisa zargin sata
Ana zargin kansilan da dagacin da hada baki wajen sace randar wutar lantarki a Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng