Equatorial Guinea: Tinubu Zai Shilla kasar Waje Kwanaki 4 bayan Gama Zanga Zanga

Equatorial Guinea: Tinubu Zai Shilla kasar Waje Kwanaki 4 bayan Gama Zanga Zanga

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta
  • Cif Ajuri Ngelale, mai ba Tinubu shawara kan yada labarai ya ce shugaban kasar zai kai ziyarar aiki ta kwanaki uku kasar Equatorial Guinea
  • Ngelale ya kara da cewa, Tinubu zai samu rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar da wasu ministocinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Laraba 14 ga watan Agusta ne ake sa ran Shugaban kasa Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Malabo a Equatorial Guinea.

An ce Tinubu zai kai ziyarar aiki Equatorial Guinea ta kwanaki uku domin girmama gayyatar da Shugaban Teodoro Obiang Nguema ya yi masa.

Kara karanta wannan

Ana sa ran Buhari ya koma Aso Rock, Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa

Tinubu zai kai ziyarar kwanaki uku kasar Equatorial Guinea
Tinubu ya samu gayyata daga shugaban Equatorial Guinea, zai kai ziyarar kwanaki uku. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu zai gana da shugaban Equatorial Guinea a fadar shugaban kasa idan ya isa, a cewar wata sanarwar da Cif Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki Equatorial Guinea

Sanarwar ta ce za a yi tarurruka tsakanin shugabannin biyu tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin mai, iskar gas da kuma tsaro.

Shugaban kasar dai zai samu rakiyar ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da wasu daga cikin ministocinsa.

A cewar Cif Ngelale, 'yan majalisar ministocin Tinubu za su shiga cikin rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da kuma nazarin damarmakin inganta alakar kasashen biyu.

Duba sanarwar, wadda @DOlusegun ya wallafa a shafinsa na X a kasa:

Tafiyar da Shugaba Tinubu ya yi zuwa kasar waje ta baya bayan nan ita ce wadda ya je kasar Ghana, inda ya halarci taron koli na tsakiyar shekara karo na shida na kungiyar AU.

Kara karanta wannan

Yadda yan adawa da kungiyoyi suka yi rubdugu ga Tinubu, aka yi batun tsige shi

Tinubu ya bar Legas zuwa Afirka ta Kudu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya bar Legas zuwa birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu domin halartar bikin rantsar da shugaban kasa Cyril Ramaphosa.

Shugaba Ramaphosa ya sake samun damar yin sabon wa'adi na mulkin kasar karkashin jam'iyyar ANC bayan babban zaben da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.