An Kama Mutumin da Yake Saida Sassan Jikin Ɗan Adam, an Same Shi da Kan Wata Mata
- An kama wani mutum mai suna Musa da ake zargi da laifin sayar da sassan jikin ɗan Adam a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya bayyana irin harkokin da yake da sassan jikin ɗan Adam yayin da ake masa tambayoyi
- An ruwaito cewa jama'an da suka kama mutumin sun damka shi ga jami'an yan sanda domin zurfafa bincike da ɗaukan mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Rahotanni na nuni da cewa an kama wani mutum dauke da kan wata mata a jihar Oyo.
Bayan an tsananta masa tambayoyi, mutumin ya fadi abin da yake aikatawa da sassan jikin ɗan Adam.
Legit ta tatttaro bayanai kan yadda aka kama mutumin mai suna Musa a cikin wani bidiyo da Oyo Affairs ta wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama Musa da kan mace
Rahotanni sun nuna cewa asirin mutumin mai suna Musa ya tonu ne yayin da yazo wucewa a yankin Amuloko dake Ibadan ta wajen wasu mutane.
Da zuwansa wajen suka ga alamun rashin gaskiya a tattare da shi kuma suka bukaci ya bude jakarsa sai suka ga kayin wata mata.
Musa na sayar da sassan dan Adam
Jaridar Punch ta wallafa cewa bayan samun Musa da kan wata mata da ba a daɗe da yankewa ba, an tsananta masa tambayoyi.
Yayin da ake masa tambayoyi, Musa furta cewa yana cikin wadanda suke sayar da sassan jikin ɗan Adam.
An mika shi a hannun 'yan sanda
Mutanen da suka kama Musa da sassan jikin na ɗan Adam sun mika shi ga rundunar yan sanda a jihar Oyo.
Ana sa ran cewa yan sanda za su tsananta bincike kan Musa da kuma gurfanar da shi a gaban alkali idan ta kama.
An kama malami da sassan dan Adam
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya ta yi nasarar cafke wani malamin addini dauke da da sassan jikin dan Adam.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama malamin mai suna Alfa Oluwafemi Idris a wani yanki a jihar Ondo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng