Shugaban APC da Aka Tsige Ya Jagoranci Gangami, Ya Hado kan Masoya Tinubu
- Rahotanni daga Fatakwal babban birnin Rivers na nuni da cewa shugaban APC na jihar da aka tsige ya shirya gangami
- An ce Tony Okocha, ya tattaro 'yan kungiyar 'Renewed Hope', suka gudanar da gangamin goyon bayan shugaban kasa
- Duk da cewa ba a san me Tony Okocha ya ke son cimmawa ba, amma an ce ya yi hakan ne domin nuna soyayya ga Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu ya barke a jihar Rivers, yayin da matasa da manya suka amsa kiran Tony Okocha.
An ce bayan tsige shi da aka yi daga shugaban APC na jihar Rivers, Tony Okocha ya kira magoya bayansa daga fadin jihar domin gudanar da gangamin.
Tsigaggen shugaban APC ya shirya gangami
A cewar rahoton Channels TV, Tony Okocha ya shirya wannan gangamin ne domin ya nunawa APC cewa yana tare da Shugaba Tinubu duk da an tsige shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Okocha a halin yanzu na jagorantar wannan gangamin a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kungiyar 'Renewed Hope' na jihar Rivers, wadanda Tony ke jagoranta daga kananan hukumomin jihar sun yi dafifi a Fatakwal.
Menene Tony Okocha ke son cimmawa?
An ce sun fito kwansu da kwarkwata suna dauke da allunan sanarwa da kuma kwalaye da ke nuna goyon baya ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ba a iya gano abin da shugaban APC da aka tsige yake son cimmawa da wannan zanga-zangar ba.
Amma dai rahotanni sun ce a halin yanzu Tony da mutanensa na tafiya kan titin Aba, inda suka haddasa cunkoson ababen hawa saboda yawansu.
Bidiyon Tony Okocha da mutanensa
Wani Femi Adewale ya wallafa bidiyon gangamin a shafinsa na Facebook, inda aka ga Tony Okocha da mutanensa suka rufe titin Aba.
Kalli bidiyon a kasa:
Kogi: Masu gangamin goyon bayan Tinubu sun bullo
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kogi ta bayyana cewa ta gano wasu matasa na shirin yin gangamin nuna goyon baya ga Bola Tinubu.
An ce matasan za su fito gangamin ne domin zama kishiya ga masu shirin zanga zangar yaki da tsadar rayuwa da ake a gwamantin Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng