Zanga Zanga Ta Haifar da Ɗa Mai Ido? Farashin Abinci da Gas na Hauhawa a Kaduna

Zanga Zanga Ta Haifar da Ɗa Mai Ido? Farashin Abinci da Gas na Hauhawa a Kaduna

  • Bayan kammala zanga-zangar kwanaki 10 a kasar nan, an fara samun hauhawar farashin kayan abinci da iskar gas a Kaduna
  • Daga cikin kayan abincin da farashinsu ya hau akwai shinkafa, wake, garin kwaki, doya da taliyar yara da wasu kayan
  • Wannan na zuwa ne bayan 'yan kasuwar Kano sun kara farashin kayan masarufi saboda jama'a sun matsu da sayen kayan abincin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Bayan kammala zanga-zangar adawa da.manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, 'yan Najeriya ba su samu saukin da su ka yi fata ba.

Tun bayan kammala zanga-zanga aka rika samun hauhawar farashin kayan abinci a wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Daga bude kasuwannin Kano bayan zanga zanga, farashi ya yi tashin gwauron zabo

Farashi
Farashin kayan abinci da iskar gas sun tsefe a Kaduna Hoto: Kypros/Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa yanzu haka, an samu karin N200 zuwa N10, 000 a kan farashin abincin daga yadda ya ke kafin zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jihar Kaduna kowane kilon makamashin gas na girki ya tashi daga N1,100-N1,200 kilo zuwa N1,400.

Yadda aka samu hauhawar farashin kayan masarufi

Mazauna jihar Kaduna sun samu sauyin farashin kayan abinci daga yadda ake sayar masu gabanin fara zanga-zangar adawa da matsin rayuwa.

A babbar kasuwar Sheikh Abubakar Rimi, ana sayar da buhun shinkafa 'yar kasar waje a kan N86,000-N90,000 sabanin N79,000 da ake sayarwa a baya.

Doya da ake sayarwa N5,000 yanzu ta koma 7,000, wake rabin kwano da ake sayarwa tsakanin N2000-2,500 yanzu ya koma N3,500.

Har garin rogo da ake kira kwaki yanzu ya koma N1,400 zuwa N1,500 daga N1,300.

An samu hauhawar farashin abinci a Kano

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

A wani labarin kun ji yadda 'yan kasuwar Kano su ka kara farashin kayan masarufi jim kaɗan bayan bude kasuwanni saboda janye dokar takaita yawo.

Yan kasuwar sun tabbatar da cewa ba sabon kaya aka sayo ba, sai dai an samu karancin su a cikin unguwanni wanda ya sa jama'a ke kara bukatar sayen kayan abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.