Albashin N70,000: Fadan Ma'aikata Zai Koma kan Gwamnoni, Za a Iya Rufe Jihohi

Albashin N70,000: Fadan Ma'aikata Zai Koma kan Gwamnoni, Za a Iya Rufe Jihohi

  • Bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da N70,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata, ana bukatar gwamnoni su fara aiwatarwa
  • Kungiyar manyan ma'aikatan kasar nan (ASCSN) ta yi barazanar daukar mataki a kan gwamnatocin jihohi da su ka ki fara aiwatar da sabon albashin
  • Sabon shugaban kungiyar, Shehu Muhammed ya ce ba za su lamunci gwamnoni su tauye hakkin ma'aikatan jihohinsu ba a daidai yanayin da ake ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati sun yi barazanar daukar mataki kan jihohin da su ka ki fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan PDP zai sauya jam'iyya, tsageru sun jefa 'bam' ofishin APP

Gwamnatin tarayya ce da amince da kara mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 bayan fafutukar kungiyoyin kwadago.

Nigeria Labour Congress HQ
Manyan ma'aikatan gwamnati za su rufe jihohin da ba su fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sabon shugaban kungiyar, Shehu Muhammed ne ya yi barazanar a Legas jim kaɗan bayan zabensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kamata ya yi gwamnoni su fara kafa kwamitocin da za su duba lamarin mafi karancin albashi da zummar fara biyan ma'aikatan jihohi a kasar nan.

Ma'aikata sun fadi muhimmanci biyan sabon albashi

Kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati ta roki gwamnatocin jihohi su yi kokarin biyan sabon mafi karancin albashi domin inganta rayuwar ma'aikata su samu sauki.

Jaridar The Sun ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Shehu Muhammed ya ce su na sane da yadda kudin da gwamnatin tarayya ke aikowa jihohi ya karu daga asusun tarayyar kasa.

Ya shawarci gwamnonin su rage kashe kudi a kan abubuwa marasa amfani domin samun damar biyan sabon mafi karancin albashin, ko a rufe jihohin baki daya.

Kara karanta wannan

Abuja da wasu jihohi 27 da har yanzu ba su kafa kwamitin aiwatar da sabon albashi ba

Gwamna zai fara biyan sabon albashi

A baya mun ruwaito cewa gwamnan Nassarawa, Abdullahi Sule ya bayyana shirin fara biyan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa bayan sahalewar gwamnatin tarayya.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Peter Ahemba ya fitar, gwamna Sule ya ce za a fara biyan N70,000 ga ma'aikata, sannan ba zai lamunci rashin gaskiya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.