An Kafa Doka, Gwamnati Za Ta Fara Kama Masu Batsa wajen Saida Maganin Gargajiya

An Kafa Doka, Gwamnati Za Ta Fara Kama Masu Batsa wajen Saida Maganin Gargajiya

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta jadda kudurinta na kawar da maganganun batsa ga masu tallan maganin gargajiya a dukkan fadin jihar
  • Kwamishina mai kula da harkokin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ne ya bayyana haka ga manema labarai
  • Legit ta tattauna da malamin addini, Muhammad Abubakar domin jin ra'ayinsa kan hukuncin da gwamnati ta dauka a jihar Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwamnati ta jaddada matakin kawo karshen kalaman batsa tsakanin masu tallen maganin gargajiya a Sokoto.

Gwamnatin ta bayyana hanyar da za ta bi wajen cafke duk mai maganin gargajiya da aka samu da karya dokar a jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fito da salon tsarin tsaro a Arewa domin maganin yan bindiga

Sokoto
An hana kalaman batsa ga masu maganin gargajiya a Sokoto. Hoto: Office of the Commissioner, Ministry for Religious Affairs, Sokoto State.
Asali: Facebook

Ma'aikatar kula da lamuran addinin ta jihar Sokoto ne ta wallafa bayani kan dokar a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu batsa wajen saida maganin gargajiya

Kwamishinan harkokin addini a jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ya bayyana cewa yan Hisbah za su fara zakulo masu yin batsa yayin tallen maganin gargajiya a jihar.

Dakta Jabir Sani Mai Hula ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukunci.

Za a hada kai da masu maganin gargajiya

Haka zalika Dakta Mai Hula ya bayyana cewa za su hada kai da masu maganin gargajiya a jihar domin cimma wannan burin.

Saboda haka kwamishinan ya mika godiya ga masu maganin gargajiya tare da cigaba da neman hadin kansu a jihar.

Maganar shugaban masu maganin gargajiya

Shugaban masu maganin gargajiya na kasa, Kabiru Muhammad na Borgu ya yi jinjina ga gwamnatin Sokoto kan daukar matakin.

Kara karanta wannan

Babu haraji: Bayani dalla dalla kan sharuddan shigo da abinci Najeriya kyauta

Shugaban ya ce za su tabbatar da cewa dokar ta yi aiki a dukkan jihohin Najeriya musamman a yankin Arewa.

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addini, Muhammad Abubakar ya zantawa Legit cewa kawo dokar a Sokoto abu ne mai muhimmanci.

Ya kuma yi kira da cewa ya kamata a kafa dokar a kowace jiha domin kawo karshen maganganun domin suna lalata tarbiyya.

Malamin ya ce ya kamata masu maganin gargajiya su san cewa duk abin da suka fada Allah zai tambayesu a kai.

Ondo: Maganin gargajiya ya kashe mutane

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar mutane akalla uku bayan shan wani maganin gargajiya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa mutanen sun sha maganin ne yayin gudanar da bikin gargajiyar da ake kira "Ibogne" a yankin Akoko a kudancin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng