Yan Sanda Sun Gano Babban Wanda Ake Zargi da Tsara 'Rusa' Najeriya Lokacin Zanga Zanga

Yan Sanda Sun Gano Babban Wanda Ake Zargi da Tsara 'Rusa' Najeriya Lokacin Zanga Zanga

  • Yan sanda sun gano wani ɗan Sudan da ya shigo Najeriya da nufin amfani da zanga-zanga wajen ruguza kasar
  • Sufetan ƴan sanda na Najeriya ya bayyana cewa wanda ake zargin yana da hannu a rikicin da ya addabi ƙasar Sudan
  • Bayanai sun nuna ƴan sanda sun kai samame hedkwatar NLC ne domin cafke wanda ake zargin amma ya gudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa rikicin da ya addabi Sudan, na cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar tsadar rayuwar da aka kammala kwanan nan a Najeriya.

Babban sufetan ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka a wurin taron matasa da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 12 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin 'bom' kan jami'an tsaro, an yi asarar rai a Najeriya

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Yan sanda sun gano babban mai kitsa ruguza Najeriya da sunan zanga zanga Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Dalilin samamen ƴan sanda a Labour House

IGP ya yi bayanin cewa jami'an ƴan sanda ba su kai samame hedkwatar ƙungiyar kwadago NLC ba, sai dai sun je wani ofis da ke cikin ginin wanda ɗan Sudan din ke zaune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Daily Trust, Kayode ya ce samamen da ƴan sandan suka kai ba shi da alaƙa da shugabannin NLC, sun je kamo ɗan ƙasar wajen da ke ɓoye a ɗaya daga cikin ofisoshin.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, wani babban jami'in ɗan sanda ya ce wanda ake zargin ya gudu amma sun ƙwato muhimman takardu.

Zanga-zanga: Ƴan sanda na kan bincike

Channels tv ta tattaro ɗan sandan na cewa:

"Mun samu bayanan sirri cewa akwai wasu miyagu da ke shirin amfani da zanga-zangar wajen ruguza ƙasar nan. Ba zan iya baku cikakken bayani ba saboda muna kan bincike."

Kara karanta wannan

Daga karshe 'yan sanda sun bayyana dalilin kai samame a hedkwatar kungiyar NLC

"Wasu daga ciki sun gudu sun bar ƙasa, wasu ma ba ƴan Najeriya ba ne, mun bi diddigin ɗaya daga ciki har zuwa Labour House. Ban san dalilin da ya sa aka yi ta surutu kan samamen da muka kai ba."
"Wani shago muka shiga wanda ɗaya daga cikin manyan masu kitsa makircin ke amfani da shi. Da shi aka rura wutar rikicin Sudan kuma ya zo ne da nufin ruguza Najeriya."

Kotu ta yi hukunci kan zanga-zanga

Ku na da labarin masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun samu nasara a kotun tarayya mai zama a Abuja a shari'ar da aka nemi dakatar da su.

Alkalin kotun ya kori ƙarar da wasu mutane 16 suka nemi a hana ci gaba da wannan zanga-zanga da aka fara saboda ana tauye masu haƙƙi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262