Shugaba Tinubu Ya Tsawaita Wa'adin Wanda Buhari Ya Ba Mukami a Gwamnatinsa

Shugaba Tinubu Ya Tsawaita Wa'adin Wanda Buhari Ya Ba Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wani naɗi a gwamnatinsa a ci gaba da jagorantar ƙasar nan da yake yi
  • Tinubu ya amince da sake naɗa Adamu Adaji a matsayin darakta-janar na hukumar kula da iyakoki ta ƙasa (NBC) a karo na biyu
  • A cewar sanarwar sake naɗin da aka yi wa Adaji, naɗin na sa zai fara aiki ne daga ranar, 7 ga watan Agustan 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sake naɗa Adamu Adaji a matsayin darakta-janar na hukumar kula da Iyakoki ta ƙasa (NBC) a karo na biyu.

An bayyana sake naɗin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

Tinubu ya yi nadi a gwamnatinsa
Shugaba Tinubu ya amince da sake nadin shugaban hukumar NBC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya naɗa shugaɓan hukumar iyakoki

Jaridar Leadership ta ce shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Efe Ovuakporie, ya ba da sanarwar ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu, ya ce amincewa da sake naɗin nasa a wa’adi na biyu kuma na ƙarshe na shekaru huɗu ya yi daidai da tanadin sashe na 16 (1) da (3) (a) na dokar kafa hukumar ta shekarar 2006, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

A cewar sanarwar, sake naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa zai fara aiki ne daga ranar, 7 ga watan Agustan 2024.

Wanene Adamu Adaji?

Adamu Adaji ya yi digirin digirgir a fannin safiyo daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma MPA a fannin harkokin gwamnati daga jami’ar Maiduguri.

Ya fara aiki a hukumar NBC ne a shekarar 1992, sannan a baya ya yi aikin koyarwa a jami'ar ABU, Zaria.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

Adamu Adaji ya kai matsayin darakta a hukumar kuma an naɗa shi babban darakta a wa’adinsa na farko a ranar 8 ga watan Agusta, 2020.

Tinubu ya ba ɗan tsohon gwamna muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo muƙami.

Tinubu ya naɗa Adebayo ne a matsayin shugaban hukumar ci gaban harkokin noma wacce aka fi sani da hukumar NALDA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng