Masu Zanga Zanga Sun Yi Gagarumar Nasara, Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci
- Masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun samu nasara a babbar kotun tarayya mai zama a Abuja a shari'ar da aka nemi dakatar da su
- Alkalin kotun ya kori ƙarar da wasu mutane 16 suka nemi a hana ci gaba da wannan zanga-zanga da aka fara saboda ana tauye masu haƙƙi
- Wannan dai na zuwa ne bayan kammala kwanaki 10 ana zanga-zanga kuma matasa sun sha alwashin ci gaba a watan Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da buƙatar hana ƴan Najeriya ci gaba da zanga-zanga mai taken #EndBadGovernance.
Kotun ta yi fatali da bukatar wanda aka nemi ta ba da umarnin wucin gadi na haramtawa kungiyoyi ci gaba da wannan zanga-zanga nan gaba a Najeriya.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Danladi Goje, Buky Abayomi, Adiza Abboda wasu mutum 13 ne suka shigar da bukatar gaban kotu ranar 12 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka nemi hana zanga-zanga?
Masu shigar da ƙarar sun nemi kotu ta tabbatar masu da ƴancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su daga barazanar masu zanga-zangar.
Lauyan masu kara, Tsembelee Sorkaa, ya faɗawa kotu cewa ’yancin rayuwa, ’yancin kai, sirri da iyali, zirga-zirga, da tattalin arzikin waɗanda yake karewa na iya fuskantar barazana saboda zanga-zangar.
Kotu ta kori ƙarar nan take
Da yake yanke hukunci, mai shari'a Lifu ya bayyana cewa zanga zangar da ake ƙorafi a kanta an gama ta a makon da ya gabata.
Ya kuma ƙara da cewa lauyan masu kara ya gaza gabatar da gamsassun shaidu da za su tabbatar da cewa masu zanga-zangar za su sake komawa kan tituna.
Mai shari'a Lafu ya ce:
"Na yi nazari kan wannan bukata kuma a gani na ba zai yiwu kotu ta amince ba, ƙorafin bai karɓu ba saboda haka kotu ta yi watsi da shi."
Daga nan ne kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga Agusta, 2024, rahoton Sahara Reporters.
'Ya kamata a sauke Bola Tinubu'
Kuna da labarin tsohon mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya ce zanga-zangar da aka yi kaɗai ta isa zama dalilin tsige Bola Ahmed Tinubu.
Lukman ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, 2024, sa'o'i 24 bayan kammala zanga-zangar kwanaki 10.
Asali: Legit.ng