Zanga Zanga: Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Mika Wadanda Su Ka Daga Tutar Rasha zuwa Abuja
- Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana nasarorin da ta samu a lokacin zanga-zangar adawa da manufofin shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Dogo Garba ya ce an cafke mutane 873 da su ake zargi da karya doka a lokacin zanga-zanga
- Daga cikin wannan adadi, rundunar ta mika mutane 76 zuwa ga hedikwatar rundunar a Abuja bisa zarginsu da daga tutar Rasha a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta damke akalla mutane 873 bisa zargin karya doka kwanakin da aka gudanar da zanga zanga a jihar.
'Yan kasar nan sun fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya daga ranar 1 Agusta, 2024 zuwa 10 Agusta, 2024.
Ta cikin sakon da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafin Facebook, kwamishinan yan sandan Kano, CP Salman Dogo Garba ya ce an damke mutanen ne da laifuka iri-iri, har da ma su daga tutar Rasha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An mika masu daga tutar Rasha Abuja
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana mika mutane 73 da ake zargi da daga tutar wata kasar yayin zanga zanga a jihar zuwa babban birnin tarayya, Abuja, Punch ta wallafa.
CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka, inda ya ce tuni aka wasu mika mutane 600 gaban kotu bisa zargin yunkurin tada zaune tsaye a yayin zanga zangar.
"A binciki masu daga tutar Rasha," Mai sharhi
Kwamred Sa'idu Bello, mai sharhi ne kan al'amuran kasa-kasa a Kano, ya shaidawa Legit cewa akwai bukatar zurfafa bincike a kan masu daga tutar Rasha lokacin zanga zanga.
Ya bayyana cewa wasu 'yan Poland da aka kama da daga tutar Rasha babbar alamar tambaya ne, ganin cewa Rasha da Poland ba su ga maciji da juna.
Amma ya ce kila 'yan Najeriya sun daga tutar ne ganin yadda su ke makwabtaka da kasashen da ke su ka samu sauki da tallafin Rasha.
An kama mai dinka tutar Rasha
A baya kun ji cewa jami'an tsaro sun damke wani matashi mai suna Ahmed bisa zargin dingawa da yada tutar kasar waje - Rasha ga sauran matasa domin dagawa a lokacin zanga-zanga.
Mazauna Arewacin kasar nan, musamman Kano, sun rika daga tutar Rasha tare da neman daukin shugaban kasar, Vladimir Putin kan halin matsin da su ke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng