WASSCE 2024: WAEC Ta Rike Sakamakon Jarabawar Dalibai 215,267, Ta Fadi Dalili

WASSCE 2024: WAEC Ta Rike Sakamakon Jarabawar Dalibai 215,267, Ta Fadi Dalili

  • A ranar Litinin, 12 ga Agusta, WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) ta 2024
  • Hukumar shirya jarabawar ta rike sakamakon dalibai 215,267 da suka zana jarabawar biyo bayan rahotannin aikata satar amsa
  • Shugaban ofishin WAEC na Najeriya Dr Amos Dangut ne ya bayyana hakan ga manema labarai tare da kuma yin karin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afrika (WAEC) ta fara fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2024.

WAEC ta rike sakamakon jarabawar dalibai 215,267 daga cikin kimanin dalibai 1,814,344 daga makarantun sakandare 22,229 a fadin kasar nan da suka zana jarrabawar.

Kara karanta wannan

WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta 2024, ta fadi yadda ake dubawa

WAEC ta yi magana yayin da ta rike sakamakon WASSCE na dalibai 215,267
WAEC ta fitar da sakamakon WASSCE ta 2024, ta rike sakamakon dalibai 215,267.
Asali: Twitter

WAEC: An rike jarabawar dalibai 215,267

Amos Josiah Dangut, shugaban WAEC na Najeriya, ya ce an rike sakamakon dalibai 215,267 saboda zarginsu da aikata laifuffukan satar jarabawa, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce adadin daliban da aka rikewa sakamakon ya ragu da kashi 4.37 daga kashi 16.29 da aka samu a WASSCE ta shekarar 2023.

An ruwaito cewa wannan adadi ya nuna kashi 11.92 na mutane 1,805,216 da suka zana jarrabawar, hukumar jarrabawar ta bayyana.

WAEC ta gargadi dalibai da makarantu

Jaridar The Punch ta ruwaito Mista Dangut ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wasu laifukan da suka shafi magudin jarrabawa.

Ya kuma bayyana cewa makarantu, masu sa ido, malamai, da daliban da ke yin irin wadannan ayyuka suna lalata tsarin ilimi.

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

An fara zana jarabawar WASSCE ta 2024 ne a ranar Talata, 30 ga Afrilu, 2024, kuma an kammala a ranar 24 ga Yuni, 2024.

Yadda ake duba sakamakon WASSCE 2024

Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar zana jarabawar kammala sakandare (WAEC) ta bayyana yadda dalibai za su iya duba sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta fitar da sanarwar ba dalibai damar duba jarawabarsu ta WASSCE a ranar Litinin, 12 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.