Bayan an Samu Tarnaki, Gaskiya ta Fito kan N573bn da Tinubu ya Turawa Gwamnoni
- Bola Ahmed Tinubu ya yi maganar makudan kudin da ya ce ya tura wa gwamnonin jihohi domin rage radadin tsadar rayuwa
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa daga bankin duniya kudin suka zo kuma ta fadi abubuwan da ya kamata ayi da su
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ci gyaran shugaban kasa kan kudin da ya ce ya tura musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi karin haske kan makudan kudin da ya ce ya tura ga gwamnonin jihohi.
Bola Tinubu ya ce ya tura kudi N573bn ga gwamnoni ne amma sai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce sam ba haka ba.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a lokacin da ya yi bayani, Bola Tinubu ya ce ya ba jihohin kudin a matsayin tallafi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
N573bn: Martanin Seyi Makinde ga Tinubu
A lokacin da Bola Tinubu ya yi jawabi bayan an barke da zanga zangar tsadar rayuwa ya ce ya ba jihohi N573bn a matsayin tallafi.
Legit ta ruwaito cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce sam kudin ba daga shugaba Bola Tinubu suka fito ba kuma ba tallafi ba ne.
Tinubu ya yi karin haske kan N573bn
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi martani kan cewa babban abin lura shi ne ko jihohi samu kudin ko akasin haka.
Bola Tinubu ya ce ba wata damuwa ko kudin daga ina suka fito, kawai buƙata ita ce gwamnonin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata.
Tinubu: 'Bankin duniya ne ya turo N573bn'
Rahoton TVC ya nuna cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa bankin duniya ne ya turo kudin a matsayin bashi ga jihohi.
Ya kuma kara da cewa an tura kudin ne a matsayin cikaton tallafin COVID-19 da shirin NG-Cares da bankin duniya ke ɗaukar nauyi.
An bukaci Tinubu ya binciki gwamnoni
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar SERAP na son shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya binciki yadda gwamnoni suka kashe bashin da suka karɓo daga bankin duniya.
Gwamnonin na jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja sun karɓo bashin $1.5bn daga bankin duniya domin rage raɗaɗin talauci ga yan kasa.
Asali: Legit.ng