Direban Adaidaita Sahu Ya Maida Jakar Kudin da Ya Tsinta, Yan Sanda Sun Sa Cigiya
- Rundunar 'yan sandan Kano ta yaba da tsantsar gaskiya da rikon amana da wani mai baburin adaidaita sahu ya nuna a jihar
- Matashin mai suna Safiyanu Mohammed ya mika wata jaka makare da kudi da ya tsinta a kwanar dakata ga rundunar 'yan sanda
- Jam'in hulda da jama'a na rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa yanzu haka ana cigiyar mai jakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Wani matashi, Safiyanu Mohammed ya dauki hankali bayan ya mayar da jaka da tsinta makare da kudi a hanyar sana'arsa ta adaidaita sahu.
Safiyanu Mohammed mai shekaru 36 ya tsinci kudin a hanyar titin Hadejia da ke kwanar Dakata, inda bai yi wata-wata ba ya mika ta ga 'yan sanda.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yaba da gaskiyar matukin adaidaita sahun ganin yawan kudin da ya dawo da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda na cigiyar mai jakar kudi
Rundunar 'yan sandan Kano ta fara cigiyar wannan jakar kudi da aka tsinta cike da kudi a kwanar Dakata da ke karamanr hukumar Nassarawa, Jaridar Leadership ta wallafa.
Wani direba, Safiyanu Mohammed dan asalin jihar Katsina, amma mazaunin Rangaza a karamar hukumar Ungogo ne ya tsinci jakar ya na aiki a ranar Juma'a.
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa babu wata alama ko lambar waya a jikin bakar jakar da makudan kudi a ciki, amma ana cigiyar mai su ya garzaya ofishin 'yan sanda da ke Bompai.
Matasahi ya mayar da kudin tsintuwa
A wani labarin kun ji cewa wani matashin mai adaidaita sahu ya mayar da wasu makudan kudi da ya tsinta ga fasinjan da ya manta kudin a baburinsa a jihar Kano.
Jim dadin mayar masa da kudinsa da yawansu ya kai Naira Miliyan 15, mai kudin dan asalin kasar Chadi ya yi wa matashin mai adaidaita sahun kyautar N400,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng