"Duk Arzikinmu?" Kashim Shettima Ya ga Rashin Dacewar Fama da Talauci a Arewa

"Duk Arzikinmu?" Kashim Shettima Ya ga Rashin Dacewar Fama da Talauci a Arewa

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa bai kamata a rika samun talauci a yankin Arewacin kasar nan ba
  • Shettima ya bayyana cewa Allah ya yiwa yankin babban arzikin da bai dace a ga talauci ya na yawo tsakanin mazauna yankin ba
  • A jawabinsa kan yadda 'yan Najeriya su ka gudanar da zanga-zanga, Shettima ya ce abin nadama ne ga al'umma da gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai yalwar arziki a yankin Arewacin Najeriya, saboda haka bai dace a rika talauci a yankin ba.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jaddada matsayarsa na cewa bai dace a rika yada labaran cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na kin Arewa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da bankadar Dan Bello, Tinubu ya dakatar da aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya ce bai dace Arewa ta yi talauci ba Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashen RFI Hausa, inda ya ba wa jama'a hakuri a kan halin matsin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnatin Tinubu ba ta fifita kudu ba" - Shettima

Kashim Shettima ya bayyana batun da ake cewa gwamantinsu ta fi mayar da hankali wajen kula da kudancin kasar nan a matsayin maganar 'yan siyasa kawai.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Kashim Shettima ya ce daga cikin ministocin kasar nan 46, gwamnatin Bola Tinubu ta nada 24 daga Arewa.

"Ka duba ma'aikatar tsaro, Minista Muhammadu Badaru Ababukar ba daga Badagry ya fito ba. Dan Babura ne a jihar Jigawa."
"Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle Maradun ba dan Mushin ba ne, dan asalin Maradun ne a Zamfara."

- Kashim Shettima

A game da batun zanga-zanga, Mai girma Shettima ya ce kowane dan kasa na da 'yancin bayyana ra'ayinsa cikin lumana.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Shettima ya kwantarwa matasa hankali, ya fadi shirin Tinubu gare su

Ganin barnar da aka jawo, mataimakin shugaban kasar ya ce abin nadama ne ga kowa.

Shettima ya fadi manufar Tinubu kan matasa

A baya mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya karbi bakuncin matasan jam'iyyar APC, tare da ba su tabbacin shirin Tinubu gare su.

Sanata Shettima ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Tinubu na ganin darajar matasa, shi ya sa ya shirya cicciba su ta hanyar ba su dukkanin tallafin da ya dace wajen cigaban rayuwarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.