An Rasa Rayuka, 'Yan Ta'addan Nijar Sun Yi wa Sojoji Kwanton Bauna a Najeriya

An Rasa Rayuka, 'Yan Ta'addan Nijar Sun Yi wa Sojoji Kwanton Bauna a Najeriya

  • An rasa rayukan jami'an sojojin Najeriya bayan ƴan ta'adda sun yi musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Gudu a Sokoto
  • Ƴan ta'addan sun hallaka sojoji huɗu tare da ƙona motocin sintiri biyu na jami'an tsaron a harin da suka kai a ranar Asabar
  • Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan masu yawa waɗanda suka fito daga jamhuriyar Nijar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Ƴan ta’adda ɗauke da miyagun makamai sun kashe sojoji huɗu a ƙaramar hukumar Gudu da ke jihar Sokoto.

Ƴan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a hanyar Kukurau zuwa Bangi yayin da suke sintiri da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Sokoto
'Yan ta'adda sun kashe sojoji hudu a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin ƴan ta'addan ya yi sanadiyyar jikkata wasu sojoji guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan ta'adda suka hallaka sojoji

Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Gudu, Yahaya Gudu, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a jiya Lahadi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Yahaya Gudu, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ce ƴan ta’addan sun kuma ƙona motocin sintiri na sojojin guda biyu.

"Eh, gaskiya ne. Wasu ƴan ta'adda sun yi wa sojoji da ke sintiri kwanton ɓauna a kan hanyar Kukurau-Bangi a ranar Asabar inda suka kashe huɗu daga cikinsu yayin da wasu biyu suka samu raunuka."
"Sun kuma ƙona motocin sintiri na sojojin."

- Yahaya Gudu

Wani mazaunin garin na Gudu wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an ga ƴan ta’addan suna tafiya a yankin a kan babura aƙalla 20 ɗauke da mutum biyu.

Kara karanta wannan

Daga karshe 'yan sanda sun bayyana dalilin kai samame a hedkwatar kungiyar NLC

Me rundunar sojoji ta ce kan harin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a daren jiya, daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce ƴan ta'addan da suka kai harin daga Jamhuriyar Nijar suke.

"An kai harin ne a kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar. A yayin gumurzun an kashe da dama daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai da alburusai.
"Gawarwakin ƴan ta'addan da aka kashe sun nuna cewa wata ƙungiyar ta'addanci daga jamhuriyar Nijar da aka fi sani da Lakurawa ce ta kawo harin. Abin baƙin ciki, an kashe jami'anmu huɗu a yayin arangamar."

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan Boko Haram mutum biyar a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar ne a kan ƴan ta'addan a wani samame da suka kai maboyarsu da ke ƙaramar hukumar Bama ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng