Cikakkken Jerin Kasashen Afirika 10 Masu Yawan Arzikin Man Fetur

Cikakkken Jerin Kasashen Afirika 10 Masu Yawan Arzikin Man Fetur

  • Ƙasar Libya wacce tattalin arziƙinta ke kan hanyar farfaɗowa ta sha gaban Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ke yawan arziƙin man fetur a duniya
  • Najeriya ta samu tagomashi inda ta ƙara yawan gangar man da take haƙowa a kowace rana daga ganga 1.28m zuwa ganga 1.7m
  • Najeriya na samun fiye da kaso 80% na kuɗaɗen shigarta daga fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje sannan babban ginshiƙi ne a kasafin kuɗinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Hukumomi a Najeriya sun sanar da cewa man fetur da ake haƙowa a ƙasar ya ƙaru daga ganga 1.7m zuwa ganga 1.28m kowace rana, wanda hakan ya sanya ta zama ta ɗaya wajen samar da man fetur a nahiyar Afirika.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki matakin tausayawa talakawa sakamakon zanga zanga

Yayin da man fetur da Najeriya ke samarwa ya ƙaru sosai saboda ƙoƙarin magance matsalar satarsa da ake yi, ta rasa matsayinta na ƙasar da ke da mafi yawan arziƙin man fetur a nahiyar Afirika.

Kasashen Afirika masu arzikin man fetur
Libaya ta zo ta daya a jerin kasashen Afirika masu yawan arzikin man fetur Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

A cewar rahoton Global Firepower, kusan ƙasashen nahiyar Afirika 10 ne suke da yawan arziƙin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙasashen Afirika 10 masu yawan arziƙin man fetur

Ga jerin ƙasashen guda 10:

1. Libya: Ganga 50bn

Libya tana a matsayi na tara cikin jerin ƙasashe 145 masu yawan arziƙin man fetur wanda rahoton GFP na shekarar 2024 ya ƙunsa.

Ita ce ta zo ta ɗaya a nahiyar Afirka.

2. Najeriya: Ganga 37bn

A cikin rahoton na GFP, Najeriya ta zo a matsayi na 11 cikin jerin ƙasashe 145 da ke da yawan arziƙin man fetur a duniya.

A nahiyar Afirika ta zama ta biyu inda take bin bayan ƙasar Libya.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake yin gargadi kan kawo cikas ga matatar man Dangote, ya ba da shawara

3. Algeria: Ganga 12.2bn

Algeria ta zo ƙasa ta uku cikin jerin ƙasashe mafi yawan arziƙin man fetur a nahiyar Afirika.

Ƙasar ta zo matsayi na 16 cikin jerin ƙasashe 145 da ke da yawan arziƙin man fetur a duniya.

4. Angola: Ganga 7.78bn

A shekarar 2024, Angola ta zo matsayi na 19 cikin jerin ƙasashe 145 da ke da mafi yawan arziƙin man fetur a duniya.

A nahiyar Afirika ta zo ta huɗu inda take a bayan Algeria.

5. Sudan: Ganga 5bn

Sudan ta zo matsayin ƙasa ta biyar da ke da mafi yawan arziƙin man fetur a nahiyar Afirika.

A cikin ƙasashe 145 da ke da shi a duniya, ta zo matsayi na 23.

6. South Sudan: Ganga 7.750bn

South Sudan ta zo a matsayi na 26 cikin jeri ƙasashe 145 da ke yawan arziƙin man fetur a duniya.

A nahiyar Afirika tana a matsayin ƙasa ta shida.

Kara karanta wannan

Daga karshe 'yan sanda sun bayyana dalilin kai samame a hedkwatar kungiyar NLC

7. Egypt: Ganga 3.3bn

Egypt ta zo matsayin ƙasa ta bakwai a cikin jerin ƙasashen nahiyar Afirika mafi yawan arziƙin man fetur.

A cikin ƙasashe 145 mafi yawan arziƙin man fetur, Egypt ta zo a matsayi na 28.

8. DRC Congo: Ganga 2.882bn

DRC Congo ta zo matsayi na 30 a cikin jerin ƙasashen duniya 145 mafi yawan arziƙin man fetur.

Ƙasar tana a matsayi na takwas a jerin ƙasashen ƙasashen Afirika 10 da ke da yawan arziƙin man fetur.

9. Uganda: Ganga 2.5bn

Ƙasar Uganda ta zo a matsayi na tara cikin jerin ƙasashen na nahiyar Afirika. Sannan ta zo a matsayi na 33 a cikin jerin ƙasashe 145 mafi yawan arziƙin man fetur a duniya.

10. Gabon: Ganga 2bn

A cikin jerin ƙasashe 145 mafi yawan arziƙin man fetur a duniya, Gabon ta zo a matsayi na 38.

A nahiyar Afirika tana a matsayi na 10.

Batun dawo da tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Ana cikin zanga zanga, Tinubu ya aika sako mai ratsa zuciya ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa an dawo da tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya cire a shekarar 2023.

Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Tinubu ya dawo da biyan tallafin fetur din ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng