Taraba: Kungiyar CAN Ta ba da Umarnin Yin Addu’o’i da Azumi Na Kwanaki 3
- Rashin ruwan sama a jihar Taraba ya tilasta al'ummar Kiristoci shirin fara addu'o'i da azumi domin neman mafita
- Kungiyar matasan CAN a jihar ita ta ba da wannan umarni yayin da amfanin gona suka fara lalalewa a fadin jihar
- Wannan umarni na zuwa ne bayan al'ummar Musulmai sun fito gudanar da addu'o'i a jihar Kano kan halin kunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta matasa a jihar Taraba ta ba da umarnin yin azumi da addu'o'i na tsawon kwanaki uku.
Kungiyar ta matasan CAN ta dauki wannan matakin ne domin neman taimakon Ubangiji saboda rashin ruwan sama da aka dade babu a jihar.
Taraba: Kiristoci sun bukaci gudanar da addu'o'i
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Lahadi 11 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Ephesian Jesse ya ce daukar matakin ya zama dole domin gyara kan laifuffukan da aka aikata, Daily Post ta tattaro.
"Ya kamata mu fito domin yin addu'o'i da kuma azumi domin neman ruwan sama, kowa ya sani yadda amfanin gona ya fara lalacewa."
"Mu yi addu'o'i ga coci-coci da suke fuskantar matsaloli domin neman kariya daga Ubangiji wanda babu abin da ya gagare shi."
"Sannan mu yi addu'a ga Gwamna Agbu Kefas domin Ubangiji ya ba shi kariya da kuma iyalansa saboda gudanar da mulki cikin nasara."
- Ephesian Jesse
Ruwan sama: An bukaci gudanar da addu'o'i
Matasan sun bukaci al'ummar Kiristoci a jihar su fara addu'o'in da kuma azumi daga gobe Litinin 12 ga watan Agusta.
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan rashin ruwan ya fara illa ga amfani gona a fadin jihar baki daya da ya tayar da hankula.
An gudanar da addu'o'i a Kano
Kun ji cewa al'ummar Musulmai sun fito domin gudanar da addu'o'i a fadin jihar Kano kan halin kunci da jama'a ke ciki.
Mazauna unguwanni da dama ne suka yi dafifi domin bin umarnin wasu malamai da al'umma da suka ce a dukufa da addu'o'i.
Asali: Legit.ng