Tsadar Rayuwa: Jigon PDP Ya Fadi Yadda Tinubu Zai Magance Matsalolin Najeriya

Tsadar Rayuwa: Jigon PDP Ya Fadi Yadda Tinubu Zai Magance Matsalolin Najeriya

  • Jigon PDP, Dare Glintstone Akinniyi, ya yi martani kan zanga-zangar da aka yi a kasar, wadda ta zo karshe a ranar 10 ga watan Agusta
  • Ya soki salon gyara tattalin Shugaba Tinubu, inda ya nuna cewa cire tallafin man fetur da karin kudin wutar lantarki suka jawo talauci
  • A tattaunawa ta musamman da Legit.ng, a ranar Asabar, Akinniyi ya fadi abin da ya kamata Tinubu ya yi domin farfado da tattalin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yayin da aka kammala zanga-zanga a fadin kasar nan, Dare Glintstone Akinni, kakakin kungiyar matasan PDP na kasa ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu.

Dare Akinniyi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba manufofinsa na gyara tattalin arziki domin rage wahalhalun da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

"Manyan Arewa da za su iya rarrashin masu zanga zanga," masoyin Tinubu ya fadi sunaye 2

Zanga-zangar yunwa: Tinubu ya samu sakon gaggawa daga jigon PDP
Bayan kammala zanga zanga, jigon PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya aika sako ga Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A cewar kakakin matasan jam'iyyar adawar, dabara ta karewa gwamnatin Tinubu don haka akwai bukatar ta nemi taimakon jam’iyyun adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ta yi magana kan zanga-zanga

A wata hira ta musamman da jaridar Legit.ng a ranar Asabar, 10 ga Agusta, Dare Flintstone Akinniyi, ya ce duk da cewa hakkin ’yan kasa ne su yi zanga-zanga, dole ne a yi a tsarin doka.

Ya yi Allah-wadai da matakin da wasu masu zanga-zangar suka dauka a arewacin kasar, yana mai cewa "dukkanmu muna da hakkin samun wannan 'yancin, amma dole ne mu kiyaye doka."

Akinniyi ya ce:

"Barnar da aka yi wa kadarori na gwamnati da na jama'a - ba za a iya kiransa da 'zaman lafiya' ba ko kuma a gan shi a zaman wani bangare na zanga-zangar lumana."

Jigon PDP ya soki jawabin Tinubu

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Manyan 'yan siyasa da kungiya da suka kushe jawabin Tinubu

Da yake karin haske game da zanga-zangar da aka yi a fadin kasar, jigon jam’iyyar PDP ya koka kan irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a karkashin kulawar Tinubu.

Ya kalubalanci matakin cire tallafin mai da karin kudin wuta, ya kuma soki Shugaba Tinubu na rashin yin magana kan matsalolin ‘yan Najeriya a jawabin da ya yi ga 'yan kasar.

Akinniyi ya ce:

“Ban taba sauraron wani jawabi marar dadi daga shugaban kasa mai ci ba sai kan Tinubu, ta yaya a doron kasa wani zai yi jawabi a kasar, ya ki fadin muhimman abubuwan da ke faruwa?"

"Ka nemi taimako" - Akinniyi ga Tinubu

Yayin da lamura ke ci gaba da tabarbarewa, jigon na PDP ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sake duba manufofinsa tare da hada kai da jam’iyyun adawa domin rage radadin da ake ciki.

Akinniyi ya ce:

"A halin yanzu, 'yan Najeriya ba sa samun saukin rayuwa, akwai bukatar gwamnati ta kira 'yan adawa domin neman taimako, dabararsu ta kare yanzu, suna bukatar taimako.

Kara karanta wannan

Bayan Legas: Matasan wata jihar Kudu sun ji kiran Tinubu, sun dakatar da zanga zanga

"Ya kamata su sake duba manufofinsu domin ragewa talaka wahalhalun da yake sha. Ba mu da matsakaitan masu kudi, ko dai kai talaka ne ko kuma mai arziki."

Zanga-zanga: Shehu Sani ya yi magana

A wani laabarin, mun ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda masu zanga-zangar yunwa Arewa ke kokarin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Sanata Sani ya cezanga-zangar ba ta shafi manufofi da shirye-shiryen gwamnati ba, kuma ba ta damu da cire tallafi ba, kawai dai yunkuri ne na karbe mulki daga hannun Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.