Gwamnoni Sun Shiga Sabuwar Matsala Bayan SERAP Ta Hada Su da Tinubu

Gwamnoni Sun Shiga Sabuwar Matsala Bayan SERAP Ta Hada Su da Tinubu

  • Ƙungiyar SERAP na son shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya binciki yadda gwamnoni suka kashe bashin da suka karɓo daga bankin duniya
  • Gwamnonin na jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja sun karɓo bashin $1.5bn daga bankin duniya domin rage raɗaɗin talauci
  • SERAP ta kuma buƙaci Shugaba Tinubu yadda aka kashe bashin $3.1bn da gwamnaatin tarayya ta karɓo daga ƙasar China

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya binciki yadda gwamnonin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja suka yi amfani da bashin da suka karɓo daga bankin duniya.

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Tinubu ya umarci ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar yadda aka kashe bashin na $1.5bn.

Kara karanta wannan

"Ba haka ba ne," Gwamna ya maida martani kan ikirarin Tinubu na rabawa jihohi N570bn

SERAP ta bukaci Tinubu ya binciki gwamnoni
SERAP ta bukaci Tinubu ya binciki gwamnoni kna bashin $1.5bn da suka ciyo Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnonin sun ciyo bashin ne domin rage raɗaɗin talauci da ƙara inganta jin daɗin al'umma a faɗin jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane bincike SERAP ke so Tinubu ya yi?

Bukatar bincikar gwamnonin da SERAP ta yi na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawale Oluwadare, wacce ta sanya a shafinta na yanar gizo.

SERAP ta kuma buƙaci Tinubu da ya umurci Fagbemi da hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar zargin karkatar da bashin $3.121bn da gwamnatin tarayya ta karɓo daga China.

"Akwai rahotannin da ke nuna cewa bashin $1.5bn da bankin duniya ya ba jihohi 36 da Abuja da bashin $3.1bn da gwamnatin tarayya ta samu daga China, an karkatar da su ko ba a san yadda aka yi da su ba."

Kara karanta wannan

NLC ta yi martani mai zafi bayan jami'an tsaro sun kai samame a hedkwatarta

"Bincike tare da tuhumar zargin cin hanci kan karkatar da bashin bankin duniya da na China, zai yi daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya."
"Mun fahimci cewa yayin da gwamna yake da kariya daga kamu ko tuhuma, ba ya da kariya daga bincike. Duk wani zargin aikata laifi kan gwamna mai ci za a iya bincike a kansa har zuwa lokacin da zai sauka sannan ya rasa kariya."
"Abubuwan da aka gano kan wannan binciken, za su iya zama silar fara shirin tsige wannan gwamnan."

- Kolawale Oluwadare

Ƙungiyar ta ba Shugaba Tinubu wa'adin kwana bakwai domin ɗaukar matakin da ya dace, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari'a idan bai yi wani abu ba.

SERAP za ta kai ƙarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiya mai kare haƙƙin tattalin arziki (SERAP) ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya janye maganar saka harajin 0.5% ga abokan hulɗar bankuna.

SERAP ta ce ƙudirin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa na 1999 wanda aka yiwa kwaskwarima kuma ya saɓawa haƙƙin ɗan Adam da na zaman ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng