Tinubu Ya ba da Umarnin Fara Biyan 'Yan Bautar Kasa N70000? NYSC Ta yi Karin Haske
- Hukumar NYSC ta karyata rahotannin da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin fara biyan 'yan bautar kasar N70,000
- Rahotanni sun karade shafukan sada zumunta cewa hukumar NYSC ta samu umarnin daga darajar asusun bankin 'yan bautar kasa
- Sai dai hukumar ta ce ba ta karbi makamancin wannan umarni daga bangaren gwamnati ba, inda ta ba 'yan bautar kasa shawara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta yi magana kan rahotonin da ke yawo cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin fara biyan 'yan bautar kasa N70,000.
Wasu rahotanni da suka rika yawo a shafukan sada zumunta sun ce hukumar NYSC ta daga darajar asusun bankunan 'yan bautar kasa domin daukar N70,000.
Sai dai a sanarwar da daraktan watsa labarai na NYSC, Eddy Megwa ya fitar a shafin hukumar na Facebook, an gano cewa rahotannin da ake yadawa ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a fara biyan 'yan NYSC N70,000?
Sanarwar Mista Eddy ta tabbatar da cewa babu wani umarni da hukumar ta samu daga fadar shugaban kasa ko wata hukumar da abin ya shafa kan wannan lamari.
Hukumar NYSC ta ce ba ta daga darajar asusun matasa masu yiwa kasa hidima ba domin fara biyansu mafi karancin albashi na N70,000.
Sanarwar ta kuma shawarci 'yan bautar kasa da su kauracewa yarda da ire-iren wadannan rahoto wadanda ake kirkirarsu domin kawo rudani ga 'yan kasar.
NYSC ta aika sako ga 'yan bautar kasa
Sanarwar ta ce:
"An ja hankalinmu kan rahoton da ake yadawa a soshiyal midiya cewa an ba da umarnin daga darajar asusun 'yan bautar kasa domin fara biyansu sabon mafi karancin albashi na N70,000.
"Wannan rahoto karya ce tsagoronta, wanda babu ko kamshin gaskiya a ciki.
“Ya kamata 'yan bautar, iyaye da sauran jama’a su lura cewa babu wani umarni da aka samu daga bangaren gwamnati kan karawa masu bautar kasar alawus."
An gargadi masu shafukan yanar gizo da su daina fitar da bayanan da suka shafi gudanar da ayyukan hukumar NYSC ba gtare da izini ba.
Gwamnati ta karawa 'yan NYSC alawus?
A wani labarin, mun ruwaito cewa rahotanni sun karade shafukan intanet cewa gwamnatin tarayya tarayya ta kara alawus ga 'yan bautar kasa daga N33,000 zuwa N77,000.
Sai dai wani bincike da muka yi, ya tabbatar da cewa babu inda gwamnatin tarayyar ta sanar da yiwa matasa masu bautar kasa karin alawus duk da cewa an kara mafi karancin albashi.
Asali: Legit.ng